Majalisar dokokin jihar Kaduna ta rattaba hannu a kasafin kudin 2020

0

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da Naira biliyan 259.25 a matsayin kassafin kudin jihar na shekara 2020.

Bisa ga kasafin gwamnati za ta kashe Naira biliyan 75.14 a matsayin kudaden da ake kashewa harkokin yau da kulum. Sannan zata kashe Naira biliyan 184.10 wajen yin manyan ayyuka a fadin jihar.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Ahmed Mohammed ya bayyana haka da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a garin Kaduna.

Mohammed ya ce gwamnati ta amince ta kara Naira biliyan takwas kan jimlar kassafin kudin da gwamnati ta fara gabatarwa.

Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin karfafa aiyukka da kawar da bukatun da wasu hukumomi da ma’aikatu a jihar suke fama da su.

“Wadannan hukumomi sun hada da hukumar RUWASSA, asibitin Barau Dikko hospital, hukumar kula da aiyukkan malamai da hukumar kula da ilimin firamare na jihar Kaduna (SUBEB).

Mohammed ya tabbatar da cewa gwamnati za ta kashe wadannan kudade ta hanyoyin da ya kamata.

Idan ba a manta ba a ranar 15 ga watan Oktoba ne mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Hadiza Balarabe ta gabatar da Naira 190.03 a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2020.

A wannan zama kakakin majalisar Aminu Shagali ya kuma amince a fara shirin samar da tallafi da aka yi wa suna ‘Sir Kashim Ibrahim Fellowship’ a jihar.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya tsara wannan shiri ne domin horas da matasa dabarun shugaban.

Share.

game da Author