Majalisar dattawa ta yi kira da a dauki matakin hana likitoci bada sakamakon gwaji na karya a kasar nan

0

A ranar Talata ne majalisar dattawa ta yi kira ga ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa da ta tsara matakan da za su taimaka wajen hana asibitoci da likitoci bada sakamakon gwaji na karya a kasar nan.

Majalisar ta kuma yi kira ga kungiyar likitocin Najeriya (NMA) da ya dauki tsauraran matakai wajen hukunta asibitoci da likitoci masu irin haka.

Zauren majalisar ta amince da haka ne bayan sanata Uche Ekwunife dake wakiltar jihar Anambra ta tsakiya ta koka da yadda asibitoci da ma’aikatan kiwon lafiya ke bada sakamakon gwaji na karya a kasar nan.

Ekwunife ta ce wannan mummunar dabi’a ya zama ruwan dare a kasar nan inda har ma’aikatan kiwon lafiya na aikata haka ne ba tare da tsoro ba ko fargaba ba ko tsoron za a iya kama su a hukunta su.

“Cikin lokaci kankani mutum zai iya samun sakamakon karya ba tare da an gwada shi ba kawai zai biya kudi ne sai a bashi.

“Illar yin haka shine bai wa mutum maganin cutar da bai kamata ba saboda sakamakon gwajin sa na karya ne.

Idan ba a manta ba a kwanaki baya ne PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda asibitocin Najeriya suka kware wajen ba mutane sakamakon gwaji na karya.

Rahotan ya nuna cewa mutane na biyan kudi a asibitocin kasar nan domin a buga musa takardar gwaji ta karya domin wadda aya na daga cikin abubuwan da ke ci wa gwamnati tuwo a kwarya.

Share.

game da Author