A ranar Laraba Majalisar Dattawa ta bayyana matukar damuwar ta dangane da yawan satar kananan yara, ta na mai cewa idan ba a yi gaggawar yin taka-tsantsan ba, to cinikin bayi na kananan yara zai barke a kasar nan.
Majalisa ta nuna wannan damuwar bayan da Sanata Barau Jibrin na APC Barau Jibrin na Kano ya shaida wa sauran dattawan majalisar cewa bukatar samo hanyar gaggauta hana wannan mummunar sana’a ta zama wajibi, domin kauce wa bata al’ummar mu mai tasowa nan gaba da kuma kauce wa batan sunan Najeriya a idon sauran kasashen duniya.
Ya yi tsinkayen cewa maida dan wani ya kasance dan wani a tilas, gudanar da ayyukan wahala na cikin gidaje, karuwanci da sauran su ke sa ake satar kananan yara a kasar nan.
Tare da goyon bayan korafin da Sanata Jibrin ya yi, sai nan take Majalisar Dattawa ta umarci Kwamitin Harkokin Mata da Inganta Matasa tare da na Shari’a, ’Yancin dan Adam da na Al’amurran Shari’a su gudanar da binciken dangane da wannan sata ta kananan yara, su bayar da shawarwari cikin makonni biyu.
Daga nan sai Majalisa ta umarci jami’an tsaron da abin ya fi shafa su tabbatar su na yin bakin kokarin ganin sun dakile yadda ake satar kananan yara da manya.
Su ma gwamnaonin jihohi horon su aka yi su karar daukar kwakkwarar matakin da zai kawo karshen daukar yaran su ana sacewa.
Ko cikin wannan makon sai da Rundunar ‘yan sanda ta bada sanarwar ceto wani karamin yaro mai shekaru 11 da haihuwa, mai suna Muhammed Ya’u, wanda aka sace a Kano tun cikin 2014, aka arce da shi Anacha.
Wannan sanarwa ta cikin wani bayani da Kakakin Yada Labarai na ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna ya sa wa hannu kuma ya raba wa manema labarai.
Haruna ya ce wasu Inyamurai ne miji da mata, Paul Onwe da matar sa mai suna Mercy Paul suka sace yaron tun cikin 2014 a Kwanar PRP, A Kano.
Sun sayar da shi kudi hannu ga wani Inyamirin mai suna Ecere Ogbodo a kan kudi naira 200,000.
“A kokarin da jami’an mu ke ci gaba da yi domin gano sauran yaran da aka sace daga Kano ana kaiwa wani sashen kasar nan, an gano wani yaro da aka sace tun cikin 2014, a Kwanar PRP, aka saida shi a garin Anacha.
“Jami’an Operatiom Puff Adder, masu dakile satar yara da garkuwa da mutane ne suka gano su.
Haruna ya ce an sake wa yaron suna zuwa Chinedu Ogbodo. Shi Ogbodo dai shi ne aka saida wa yaron kan kudi naira 200,000.
Ya ce a yanzu haka ana ci gaba da binciken wadanda ake zargin su uku. Kuma ana ci gaba da kokarin ceto sauran yaran da aka yi ikirarin an sace a Kano.
Ya kuma gode wa jama’a dangane da irin gudummawar da suke bayarwa wajen kokarin ceto sauran yaran.
Wannan ne karo na uku da aka gano yaran da ake sacewa daga Kano ana saidawa a jihohin Inyamurai.
Yaran farko da aka fara ganowa su 9 ne. Daga baya kuma an gano wasu yara biyu da aka sace daga Jihar Gombe, sai kuma wasu yaran da aka sata daga Jihar Kebbi
Discussion about this post