Mahara sun kashe mutane 18 a jihar Zamfara

0

A ranar lahadi da karfe biyar na yamma wasu mahara suka kai wa kauyen Karaye dake karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara hari.

Mazauna kauyen Karaye sun bayyana cewa maharan sun kashe mutane da dama a kauyen domin sun far wa kauyen ne suna ta aman wuta kawai da manyan bindigogi wuta har na tsawon awa daya ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba.

A wani takarda da ya fito daga rundunar sojin Najeriya wanda PREMIUM TIMES ta samu ya nuna cewa akalla mutane 18 ne suka rasu a wannan harin.

Wani likita a babban asibitin gwamnati dake Gummi ya ce an kawo gawar mutane 20 sannan har yanzu ana ci gaba da kawo wasu asibitin.

Bayan haka mai taimaka wa gwamna Bello Matawalle kan harkokin tsaro Abubakar Dauran ya bayyana cewa wasu Fulani ne suka kai harin daukar fansan rayukan ‘yan uwan su da aka kashe a kwanakin baya.

Makoni biyu da suka gabata wasu ‘yan kungiyar sakai daga kauyen Karaye sun kashe wasu Fulani a Kasuwar Bardoki.

Dauran yace tsoffi da dama ne aka kashe a wannan hari.

A dalilin haka gwamnati ta hana duk aiyukkan kungiyar ‘yan sa kai a jihar sannan ta kama duk wadanda ke da hannu a kashe wadannan Fulani.

Dauran ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankalinsu cewa gwamnati na kokarin kawo karshen wannan matsala.

Har yanzu dai rundunar sojin Najeriya batace komai ba game da abin da ya faru.

Share.

game da Author