Wasu da ake zaton ‘yan bindiga sun baiwa wani makarantan sakandare dake garin Jangebe, Karamar hukumar Talatan Mafara hutun dole har na tsawon makonni biyu, kowa ya zauna a gida kawai.
Cikin dalibai da na malaman wannan makaranta duk sun duri ruwa inda kakaf suka kaurace wa makarantar ranar Juma’a 1 ga watan Nuwamba wanda daga ranar ne dokar maharan zai fara aiki.
An dai waye gari ne aka ga wani takarda manne a kofar ofishin shugaban makarantar an runuta cewa ” Daga ranar 1 ga watan Nuwamba kada wani dalibi ko malami ya sake zuwa makarantan nan har sai bayan kwanaki 14.”
Hakan yasa tuni dai dalibai da malamai suka bi wannan umarni suka kaurace wa makarantar.
Saidai kuma wasu suna ganin ‘yan bindiga ne suka manna wannan takarda domin a ciki sun rubuta cewa idan ba abi wannan umarni ba to lallai za su babbake makarantar kaf.
Rundunar Soji da ke aikin samar da tsaro a jihar Zamfara sun ce suna nazarin wannan wasika na barazana da aka aika wannan makaranta sannan zara bi diddigin abin.
Discussion about this post