Fitattun ‘yan wasan fina-finan Hausa Rahama Sadau da Fati Washa sun lashe manyan Kyautuka a bikin bada kyaututtuka da aka yi Landan, Kasar Ingila.
Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar shekara ta 2019 da fim din Sadauki.
Ta doke abokanan sana’ar ta da suka shiga gasar, Halima Ateteh da Aisha Tsamiya.
Ita ma Rahama Sadau da Ali Nuhu sun karbi kyautuka na jaruman fina-finai a Najeriya.
Dubban masoyan wadannan jarumai sun yi tururuwa a shafukan jaruman domin taya su murna game da wannan karramawa da aka yi musu.
Fati Washa ta godewa masoyanta tana mai cewa zata ci gaba da fitowa a fina-finan da za su nishadantar dasu sannan da zasu rika alfahari da ita.
Haka ita ma Rahama Sadau ta gode wa wadanda suka shirya wannan biki na mika kyaututtuka ga jarumai sannan ta godewa wa masoyanta a ko ina a fadin duniya.
An yi wannan biki na kareama jaruman Fina-finan Najeriya ne a garin Landan, Kasar Birtaniya.
Sai dai kuma duk da an kammala wannan taro jaruman sun rika saka hotunan su suna shakatawa a tituna da wuraren hutawa dake birnin Landan.
Tare da jaruman, fitacciyar ‘yar wasan Hausa, Hadiza Gabon ita ma an gansu tare a duka hotunan da suke ta sakawa a shafunan su.
Wannan shine babban karramawa da aka taba baiwa Fati Washa a wajen kasa Najeriya.
Abokanan aikinta da dama da masoyanta suna yaba mata saboda dattaku da kama kai da take da shi a harkokin ta a farfajiyar fina-finan Kannywood.