Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya bayyana cewa albarkar da aka samu a fannin noma shinkafa a wannan daminar zai taimaka kwarai wajen karyar da farashin shinkafa, ta yi arha takyaf.
Bagudu wanda shi ne Shugaba Kwamitin Shugaban Kasa na Noman Shinkafa da Alkama, ya yi wannan jawabi ne a yau Litinin a garin Argungu, jihar Kebbi, a lokacin da ya ke taron ganawa da manoman shinkafa na yankin.
“Albarkar noman da aka samu a wannan damina zai rage tsadar shinkafar da mu ke nomawa a nan gida, kuma hakan zai kara rage bukatar shigo da ta fasa-kwauri a cikin kasar nan. Sannan kuma ta nan gida za ta yi arhar da duk irin talaucin mutum ba zai kasa sayen ta ba.” Inji Bagudu.
Bagudu ya kuma shaida wa manonan cewa gwamnatin sa nan ba da dadewa ba za ta shigo da kananan injinan casar shinkafa ta raba su manoman domin karfafa ingancin shinkafar da manoman ke cashewa su na kai wa kasuwanni.
“Tuni dai an rigaya an horas da matasa yadda za su rika sarrafa wadannan injina da za mu raba a dukkan kananan hukumomi 21 na wannan jihar.” Inji Bagudu a wurin taron.
Mawi manomi mai suna Abubakar Usman, ya shaida wa gwamna cewa sun samu shinkafa mai tarin yawa a bana, kuma su na so a shekara mai zuwa ma albarakar noman ta su ta wuce wadda suka samu a bana.
Sai dai kuma ya roki gwamna cewa gwamnatin jihar Kebbi ta tallafa musu da takin zamani, maganin kashe kwari da kuma injinan casar shinkafa.
Discussion about this post