Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kwaikwayon dabi’un Turawan Yamma ne ya gurbata al’adun Afrika, har ta kai a yanzu an daina ganin girman dattawa.
Buhari yayi wannan kalami a ranar Litinin, da ya ke jawabi a taron Kasahen ECOWAS kan ‘yancin dattawa masu matsanancin shekaru.
Da ya ke magana ta bakin wakilin sa, George Akumeh, Buhari ya roki Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS ta fito da tsarin da zai rika tallafa wa dattawa masu matsanancin shekaru.
Buhari wanda ya ce dabi’ar mutanen Afrika ce girmama dattawa, amma a yanzu hakan sai kara tabarbarewa ya ke yi, saboda cudanya da dabi’un Turawa.
Daga nan sai ya ci gaba da kira ga ‘yan Afrika su ci gaba da yin riko ga al’ada da dabi’ar ganin girman dattawa. Ya ce, “saboda idan ba mu yi haka da kan mu ba, to ba za mu zauna wasu su zo su yi mana hakan ba.
Buhari ya ci gaba da cewa, “akwai bukatar mu farka daga barci, mu mike tsaye mu tunkari wannan kalubale na girmama dattawa a yankin Afrika ta Yamma.
“Akwai kuma bukatar mu hada kai da sauran kashen wannan yanki da ma sauran kasashen duniya domin mu kwato wa dattawa ‘yancin su a fadin duniya.”
Daga nan sai ya bayyana wasu matakai da Najeriya ta dauka domin shawo kan wannan kalubale na ‘yancin dattawa masu matsanancin shekaru.
Daga ciki kuwa har da Dokar Galihun Dattawa ta 2018, wadda ta halasta ba su kudaden sun a fansho bayan ritaya.
Ya kuma ce gwamnati na nan na duba yiwuwar rika samar wa dattawa masu matsanacin shekaru magunguna a farashi mai saukin gaske.