Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ya yi kira ga gwamnati da ta kafa asusun musamman domin inganta kiwon lafiyar a kasan.
Shugaban kwamitin likitocin da suka kware a daukan hoto ‘Radiologist’ Ododo Bernard ne ya fadi haka a taron da kungiyar na shiyar a Abuja.
Duk ranar 8 ga watan Nuwanba ne kungiyar likitocin da suka kware a daukan hoton jikin mutum tare da kungiyar NMA suke haduwa domin tattauna hanyoyin inganta aiyukkansu da fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Bernard yace irin wannan asusun da gwamnati za ta kafa zai rika aiki ne kamar yadda hukumar tallafawa Jami’o’I wato TETFund take yi a kasan.
Ya ce yin haka zai taimaka wajen samar da ingantattun kayan aiki na zamani a asibitocin kasar nan.
“ Kada fa a manta cewa duk kwarewar ma’aikacin kiwon lafiya idan babu ingantattun kayan aiki kwarewarsa zai zama na banza domin duk gwajin da aka yi zai zama ba daidai ba wanda hakan zai sa a ba mara lafiya maganin cutar da ba haka ba.
Bayan haka Bernard ya kuma koka kan yadda likitoci musamman wadanda suka kware a wajen daukan hotan jikin mutum suke ficewa zuwa kasashen waje domin yin aiki.
Daga nan sai yayi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar kiowon lafiyar kasar nan da su matso kusa a hada hannu domin inganta kiwon lafiyar mutanen kasar nan sannan kuma da kuma inganta ayyukan ma’aiakatan kiwon lafiya a Najeriya domin rage yawa-ywan waske wa kasasshen waje da suke yi.
Discussion about this post