Ranar Larabar da ta wuce ne Majalisar Dattawa ta yi wa kudirin dokar soshiyal midiya karatu na biyu.
An kirkiro kudirin dokar domin a dakile watsa labaran karya a soshiyal midiya.
Wa Ya Kirkiro Kudirin Dokar Soshiyal Midiya?
Kudirin mai suna ‘Kudirin Neman Kafa Dokar Watsa Labaran Karya na 2019, Sanata Mohammed Musa ne daga Jihar Neja ya kirkiro shi, kuma ya gabatar da shi a Majalisar Dattawa makonni biyu da suka gabata.
Tun bayan kirkiro shi dai jama’a da daman a ta yi wa kudirin tsinuwa, musamman daga masu tu’ammali da intanet.
Dama kuma an yi irin wannan kokarin a lokacin majalisar Bukola Saraki, amma shi Saraki bai goyi bayan a kafa dokar ba.
Shi Musa wanda ya sake kawo wani kudirin na yi wa soshiyal midiya talala, y ace ba nema ya ke a yi wa soshiyal midiya takunkumi ba.
Amma dai ya ce tabbas ya na so a shawo kan yada labarai na karya, kagaggu kuma marasa sahihan tushe a intanet.
“Ni ina ganin wata dama ce aka zamu domin a magance matsalar wannan barazana, domin idan ba a gaggauta magance ta ba, to fa za ta iya gurbata tsarin siyasa da kuma yanayin zamantakewar tare a kasar nan.” Inji sanatan da ya kawo wannan kudiri.
Yaya Kudirin Dokar Soshiyal Midiya Ya Ke?
Shi wannan kudiri ne da ake so Majalisa ta maida shi ya zama doka, domin hana watsa labarai na karya, bogi, jabu, kazafi da kuma yarfe a soshiyal midiya.
Domin a dakile watsa karairayi da kuma hukunta masu watsa wadannan labarai, wanda yin hakan zai zaftace sadarwa da saoshiyal midiya baki daya.
Manufa
Matakan da za a dauka sun hada da kawai da labaran karya daga soshiyal midiya da kuma hana daukar nauyi ko kashe wa kafar da ke watsa labarai na karya kudade.
Ana so duk wani abu da aka buga na siyasa, to ya kasance fosta ce main dauke da cikakkun bayanai.
Za A Hana Watsa
i. Duk wani abin da zai kawo wa harkar tsaron Najeriya cikas ko wata barazana.
ii. Duk wani abu da zai iya kawo wa harkar kiwon lafiya ko kudin Najeriya barazana da sauran su a Najeriya.
iii. Duk wani abin da zai kawo barazana ga huldar diflomasiyyar Najeriya da wasu ko wata kasa.
iv. Duk wani bayani zai iya kawo cikar ga alkaluman zaben wani dan takara a lokacin zabe.
v. Duk wani abin da zai haddasa gaba da kiyayya tsakanin al’umma ko tsakani wani mutum da mutum.
Me Ke Hukuncin Karya Doka
Za a ci tarar naira 300,000 ga wanda ya karya doka, ko kuma daurin shekara uku.
Haka shi mai shafin intanet ko na facebook, ko instagram ko twitter, ko ma wane ne, za a ci ma shafin wannan tarar ko wannan hukuncin.
Za A Hana Bude Shafukan Intanet Ana Watsa Karairayi
Duk wanda ya bude za a ci shi tarar naira 200,000 ko daurin shekaru uku a kurkuku.
Idan kuwa an watsa bayanan alkaluman zabe na karya, to tarar naira 300,000 ce za a yi wa mai shafin.
Idan kafafen yada labarai na Online ne suka watsa labaran karya, za a umarci su buga jawabin bada hakuri. Idan suka ki kuwa, za a ci tarar su har naira milyan 5.
Za a nemi Hukumar Kula Da Sadarwa ta Kasa ta kulle kafar intanet da aka samu ta na watsa bayanai na karya.