KOWA DA RANAR SA: Yadda ‘Yan Jagaliya da Sara-suka su ka yi rana a zaben Kogi

0

Fitowa suka yi gaban su gadi domin a-yi-ta-ta-kare. Sai da su ka nuske da kayan maye sannan su ka fito domin kaddamar wa mai tsautsayi ko mai karar kwana.

Bindigar maharba da ta mayaka. Adda. Gariyo. Barandami. Kurada. Gatari. Gorori. Sanduna. Wukake. Asake. Rodi. Rassan itace da falankan katako. Hatta ruwan duwatsu da ma duk wani abin da hannu zai iya dauka a yi amfani da shi, duk an yi amfani da su wajen hargitsa zaben Gwamna da na Sanata a Jihar Kogi.

Ratatata! Tatatata! Faf-faf-faf-faf! Kara ce ta fitar aman harsasan bindiga samfurin AK47, bindigar nan da wanda ya kera ta, Anatoliv Kloshinakov, daga baya ya yi da-nasanin wannan fasaha da ya yi, saboda irin yadda ake ake amfani da ita wajen daukar ran dan Adam, wanda bai ji ba bai gani ba.

Da wanda ya ji, da wanda ya gani, da wanda bai ji ba, kuma bai gani ba, sun firgita kuma sun rika arcewa yayin da karar harbin bindigogi ya rika tashi a rumfunan zabe daban-daban a lokacin zaben Gwamnan Jihar Kogi, a ranar Asabar da ta gabata.

Ruwan duwatsun da shaidanun matasa ‘yan jagaliya suka rika antayawa a rumfar zaben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Musa Wada, kai ka ce tara su aka yi domin su yi atisayen jifar-shaidan a biya su.

Ba babba ba yaro, ba mace ko namiji, ba mai kaki ba mai falmara ko mai tagiya. Duk wanda ya ji ratatata, tatatata ko faf-faf-faf-faf, sai dai ka ga ya fice a guje. Kama daga jami’in zabe zuwa ’yan sa-ido, ’yan jarida da ‘yankucukullun kananan yara masu talla duk rika rantawa a na kare kowa na neman mabuya.

Takalma. Jakar hannu da ta ratarawa a wuya ko ta sarkafawa da goya a gadon baya. Wayoyin hannu. Katinan jefa kuri’a. Takardun lissafin yawan kuri’u. Akwatina zabe. Kujeri da tebura. Robar ruwan sha da ledojin ‘pure water’. Makullan motoci. Hatta hulunan hana-sallah, duk an gudu an bar su, an tattake su, a yayin gudun tsere wa harsasan da aka rika ratattakawa a wuraren zabe daban-daban, a kananan hukumomi daban-daban.

Wasu sun karye, wasu sun goce. Wasu sun samu targade wasu kuma an musu rotse. An sari wasu an yanki wasu. Wasu sun sha duka da gora ko sanduna. Wasu ma da falankin katato aka rika faskar su.

Ba Najeriya kadai ba, duk duniya an san an yi ratatata a zaben Jihar Kogi. Shugaban Kasa ya sa nan yi ratatata. Malamai sun san an yi ratatata. Gwamna Yahaya Bello ya tabbatar da an yi ratatata.

Ratatata! Wannan alama ta sautin zabarin karar fitar har sasashen bindiga, yanzu ta zama abin alfahari ga matan jam’iyyar APC na Jihar Kogi.

An nuno su sanye da kaya masu launin atamfa mai hoton Gwamna Yahaya Bello, su na rawar murnar cin zabe ‘ta hanyar ratatata.’

“Dem go hia am, am go hia am, tatatata. Dem go hia am ratatata!” Ma’ana, “Sai dai su ka rika jin ana harbi tatatata. Sai dai suka rika jin harbi ratatata. Haka su ke wakar, sun a rawa, su na murna, lokacin da masu kidan caki da akayau da rabajau ke musu kida su kuma matan na rawa da waka, cikin tinkaho da murna da galatsi, har ma da ana nuno wasun su na yi wa mutane gwalo.

Wannan bidiyon a yanzu shi ne ke yawo a ‘soshiyal midiya’, kowa na kallo. Mai mamaki na yi, mai takaici na yi, mai Allah-wadai ma shi na yi.
Daga cikin wadanda aka ratattaka wa harbi aka kashe, har da dan uwan Sanata Dino Melaye. ‘Yan sanda sun tabbatar da an yi tashe-tashen hankula. Rahotanni sun ce ann kashe mutum 10, an ji wa 129 raunuka.

Wannan duk bai isa ba, sai da aka iske wata Shugaban Bangaren Matan Jam’iyyar APC aka wata wa gidan ta wuta, aka banka masa wuta. Ita da gidan duk sun kone kurmus.

Duk wannan abubuwa da suka faru, Gwamna Yahaya Bello ya tabbatar da cewa tashe-tashen hankulan ba su kai yadda har za a rika kushe zaben ana cewa bai inganta ba.

Shugaba Muhammadu Buhari da kan sa ya taya Yahaya Bello murna, a wannan zabe da aka fara yin ratatata tun kafin ranar zabe. Aka banka wa Ofishin Jam’iyyar APC na Jiha wuta, a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.

Tun bayan kammala zaben dai zukatan ‘yan Najeriya da dama sun yi sanyi. Da yawa sun ce ba su kara yin zabe. Wasu kuwa tsine wa dimokradiyya kawai su ke yi. Wasu na ganin cewa najasar da APC ta yi alkawarin gyarawa idan ta ci zabe, sai ma ta kara jaddada ta, har ta kai ga shigo da ratatata a cikin ‘shika-shikan’ cin zabe.

Dan takarar gwamna na PDP, Musa Wada dai ya ce shi ‘ba wawa’ ba ne da zai taya Yahaya Bello murna, ko ya amince da zaben.

Hausawa da dai sun ce kowa ya yi zagi a kasuwa, to ya san da wanda ya ke. Ko da kuwa ya yi wannan zabi bayan ya ji tashin karar harsashen bindiga–ratatata!

Share.

game da Author