Kotun dake Karu, Abuja ta yanke wa Joy Alake hukuncin share harabar kotu na tsawon makonni biyu a dalilin sace turaman zannuwa tara da siket biyu a shagon wata mata.
‘Yan sanda sun kama Joy da wadannan kaya wanda kudin su ya kai Naira 68,000 bayan mai shagon, Rosemary Akande ta kawo kara a ofishin su dake Karu.
Dan sandan da ya shigar da karar mai suna Vincent Osuji yace a ranar 30 ga watan Oktoba Rosemary ta kawo karar satar da aka yi mata a shago.
Rosemary ta ce an sace mata turaman zannuwa tara da siket biyu a shagon ta sanna ta ce ta zargi wata mata mai suna Joy Alake da yi mata wannan sata.
Osuji yace bayan sun gudanar da bincike ne sai suka kama Joy da wannan kaya. Ita da kanta ta ce ta sace su daga shagon wannan mata.
Alkalin kotun Sani Mohammed bayan yin watsi da rokon sassauci da Joy ta nema ya yanke mata hukuncin za ta rika share harabar kotun kullum da safe har na tsawon makonni biyu.