Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, ta hana EFCC ci gaba da gurfanar da tsohon Shugaban Hukumar Kwastan ta Kasa, Dikko Inde a Kotu.
Inde, dan asalin Jihar Katsina, ya yi shugabancin kwastan a zamanin mulkin Goodluck Jonathan.
Ana zargin sa da karkatar da naira bilyan 1 wadda aka ware domin gina makarantu da asibitoci ga jami’an kwastan, amma Inde ya kwashe kudaden, ya gina fankamemen gida da su.
Mai Shari’a Nnamdi Dimgba ne ya amince da rokon da Inde ya shigar a kotun sa, inda ya nemi a hana EFCC ci gaba da gurfanar da shi kotu, domin akwai yarjejeniyar da ya kulla tsakanin sa da gwamnatin tarayya.
Mai Shari’a Dimgba ya ce tunda akwai yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Dikko Inde da Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, cewa kada a ci gaba da gurfanar da shi, don haka babu wani hurumin da EFCC za ta ci gaba da maka shi kotu.
Wannan yarjejeniya tsakanin Dikko da Ministan Shari’a Abubakar Malami, an yi ta ne a bisa cewa Dikko Inde zai maida wa gwamnati naira bilyan 1.5 na kudaden da ya sata a lokacin da ya ke shugabancin hukumar kwastan ta kasa.
Mai Shari’a Dimgba, ya ce dokar kasa ta Sashe na 174 ta bai wa Ministan Shari’a karfin ikon kulla irin wannan yarjejeniyar.
Idan ba a manta ba, ba da dadewa ba bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki, an kwace manyan motocin alfama masu tsada guda 17 da aka samu an fufe cikin manyan dakuna a wani babban gidan Dikko Inde da ke Kaduna.
Wasu rahotannin ma sun ce motoci 125 ne aka kwace daga hannun sa.