Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa sauya fasalin Najeriya abu ne da tilas sai ya faru, ko ba-dade, ko ba-jima, matukar dai ana so Najeriya ta ci gaba.
Fayemi, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke gabatar da wata takarda wurin wani taro a Cibiyar Jaddada Zaman Lafiya, USIP, a Birnin Washington DC, Amurka.
Cikakken jawabin da Fayemi ya gabatar na kunshe cikin sakon wata takarda da Kakakin Yada Labarai na gwamnan, Olayinka Oyebode ya aiko wa PREMIUM TIMES.
‘Yan Najeriya da dama, ciki har da babban dan adawa, Atiku Abubakar sun sha kiraye-kirayen cewa a sauya fasalin Najeriya, ta yadda za a karkasa wasu bangarorin iko daga tarayya zuwa wasu sassa.
Sai dai kuma wadannan kiraye-kiraye duk Shugaba Muhammadu Buhar ya yi watsi da su, tare da tsayuwa kyam cewa ba dole sai an sake fasalin Najeriya ba.
Shi ma Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya goyi bayan sake fasalin kasar nan, har ma ya rika yin kira da a kirkoro ‘yan sanda na jihohi.
Amma kuma Shugaba Buhari bai gamsu da wannan shawara ya kafa jami’an ’yan sandan jiha ba.
Fayemi ya kara da cewa a cikin Kudirorin Jam’iyyar APC na 2015 da 2019, duk akwai batun sake fasalin kasar nan idan APC din ta ci zabe.
Ya ce kuma ana kan wannan batu, domin a gyara yanayin rashin raba-daidai-gwargwado da ake ci gaba da gudanarwa a tafiyar da Najeriya.
Daga nan ya yi kira ga ’yan Najeriya su rika nuna wa shugabanni laifin su, tare da bin-diddigin duk irin shugabancin da ake yi musu.
Cikin wadanda suka halarci taron har da tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, Farfesa Attahiru Jega, Gwamna Samuel Ortom na Benuwai, Minista Aishatu Dikku da sauran wasu da dama.
Mutane da daman a ganin cewa ‘yan Arewa ne bas u so a gyara fasalin Najeriya, saboda kudaden fetur da jihohin Arewa ke zamu, za su iya raguwa zuwa cikin cokali.