KARIN ALBASHI: Ko gwamnoni su biya mu ko su sauka kawai -NLC

0

Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ta bayyana cewa ya zama wajibi Majalisun Dokoki na Jihohi su tilasta wa gwamnonin jihar su domin su biya karin albashi ga ma’aikatan kowace jiha.

Babban Sakataren NLC na Kasa, Emmanuel Ugboaja ne ya yi wannan kira a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a jiya Lahadi, a Lagos.
Ugboaja ya ce duk gwamnan da ya ki biyan karin albashi, to gaggauta tsige shi kawai.

Sakataren na Kungiyar Kwadago ta Najeriya, ya shaida wa manema labarai cewa gwamnonin kasar nan sun bayyana cewa ba za su iya biyan fiye da karfin kowace jiha ba.

Sai dai kuma NLC ta ce babu wani dalilin da zai sa gwamnoni su yi korafi a kan biyan naira 30,000 mafi kankantar albashi.
Ya ce kowace jiha ta na da karfin biyan karin albashi.

“Laifi ne babba ga kasar nan idan har wani gwamna ya murje idon sa ya ce eai ba zai iya biyan karin albashi ba.

“Amma wasu daga cikin wadannan gwamnonin shatar jirgin sama su ke dauka a duk inda za su tai. Shi wannan ai su na da kudin biya ko?

Daga nan sai ya yi murna da nuna goyon bayan kafa Majalisar Shawara da Tuntuba ta Kwadago da aka kafa, wadda ya ce za ta taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakanin duk wani sabani, rashin fahimta da kuma tankiya tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago.

Ya kuma yi kira ga gwamnatinn tarayya da ta dauki tsatstsauran mataki ga duk wata hukumar da ta ki biyan ma’aikata.

Sama da shekara daya kenan ana sa-toka-sa-katsi a kan batun biyan karin albashin ma’aikata a kasar nan. Amma har yau bai kankama ka-in da na’in ba.

Share.

game da Author