Jam’iyyar APC ta “dakatar” da Oshiomhole

0

Jam’iyyar APC reshen jihar Edo ta takatar da shugaban jam’iyyar na Kasa, Adams Oshiomhole daga jam’iyyar.

A sanarwar dakatarwar da ta fito daga fadar gwamnatin jihar dake Benin, shugabanin jam’iyyar APC na kananan hukumomi 18 dake jihar suka rattaba hannu a dakatar da Oshiomhole.

Dukkan su sun ce shugabannin jam’iyyar sun ce shugaban jam’iyyar na kasa wanda dan asalin jihar kuma tsohon gwamnan jihar Oshiomhole ne ummul-aba-isan rikita-rikitar da jam’iyyar ta fada tsundum a ciki yanzu a jihar.

” Adam Oshiomhole ne ya kirkiro duk rikice-rikicen da ake fama da su a jam’iyyar a jihar, a dalilin haka kuwa, muna nuna bacin ran mu akan haka sannan da dakatar dashi daga jam’iyyar a jihar.”

” Muna tsoron kada abinda ya faru a jihar Zamfara ya faru a jihar mu domin salon da Oshiomhole ya dauka kenan.”

Idan ba a manta ba ba a ga maciji a tsakanin gwamnan jihar Edo, Obasaike da shugaban jam’iyyar na Kasa Adam Oshiomhole duk da ko daga jiha daya suke.

” Rikicin yau da bam da na gobe.”

Shugaban jam’iyyar Anselm Ojezua, da mataimakin sakataren jam’iyyar Ikuenobe Anthony, ne suka saka wa wannan takardar dakatarwa hannu.

Share.

game da Author