JAJIBIRIN ZABE: Majalisar Dattawa ta amince a bai wa Jihar Kogi naira bilyan 10

0

Majalisar Dattawa ta amince a bai wa Jihar Kogi naira bilyan 10.069 a matsayin kudaden da gwamnatin tarayya za ta biya ta na ayyukan da ta yi, wadanda tarayya din ce ya kamata ta yi ayyukan.

Amincewar ta biyo bayan karbar shawarar Rahoton Kwamitin Nazarin Basussuka da Kwangilolin da ya kamata a biya ga jihohi ya gabatar wa majalisa.

Za a damka wa Kogi takardar yarjejeniyar alkawarin biyan ta wannan adadin kudin ne na ayyukan da ta gudanar. Sai dai kuma takardar alkawarin na da muhimmancin da idan aka nuna ta banki, to nan take za a iya karbar ramce makudan kudade a banki, kafin wa’adin ranar biyan kudin ga jihar Kogi.

A ranar 15 Ga Oktoba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta amince a bai wa Kogi wannan adadin kudade har naira bilyan 10.069.

Ya ce Majalisar Dattawa zango na 8 da ta shude ce ta rattaba amincewa a bai wa wasu jihohi 24 daga cikin 25 kudaden, amma ba ta amince a bai wa Kogi a lokacin ba.
Kudaden dai Buhari ya ce kudade ne na ramuwar biyan wasu ayyuka da jihohi ke yi a madadin gwamnatin tarayya.

Shugaban Kwamiti Clifford Ordia ne ya mika rahoton amincewa a biya kudaden bayan ya gana da Manyan Sakatarorin Ma’aikatar Kudade da na Ayyuka da Gidaje.
Kwamitin kuma ya zauna da wakilai daga ma’aikatar kudade da ayyuka da gidaje na jihar Kogi.

Ordia ya kara da cewa sun zagaya sun ga tinana guda bakwai na gwamnatin tarayya da Kogi ta gina. Wannan ne ya sa aka amince a biya kudin.

Sai dai kuma kafin a amince da biyan kudaden, Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya nuna kin amincewa da bada kudaden.

Ya ce ba daidai ba ne a biya kudaden domin bai fi saura kwanaki biyu ba kacal a gudanar da zaben gwamna a Jihar ta Kogi.

Daga nan sai ya bayar da shawarar cewa a dakatar da biyan kudaden har sai bayan zabe da sati daya.

Ya ce ya na bada wannan shawara ne don kada a yi amfanin da kudaden ta hanyar da ba ta dace ba, musamman aikata gararumar zabe.

Share.

game da Author