INKONKULUSIB: Zaben Dino da Smart bai kammalu ba, sai an sake – Hukumar Zabe

0

Hukumar zabe ta bayyana cewa zaben kujerar sanata ta Kogi ta Yamma bai kammalu ba.

Malamin zabe da ya bayyana sakamakon zaben ya bayyana cewa kuri’un da aka soke sun fi yawan kuri’un da Adeyemi Smart ya lashe zaben da shi.

Shi dai Smart na jam’iyyar APC ya fi yawan kuri’u a zaben. Ya samu zunzurutun kuri’u 80,118, shi kuma Dino na PDP ya samu kuri’u 59,548.

Smart ya ba Dino ratar kuri’u 20,570.

Sai dai kuma malamin zabe ya bayyana cewa an samu matsaloli da 53 da ke da yawan wadanda suka yi rajistan zabe 43,127.

A bisa wannan dalili ya sa ba za aiya bayyana Smart da ya ke da yawan kuri’u ba a matsayin wanda yayi nasar a zaben.

Hukumar zabe ta ce za a sake zabe a wadannan mazabu da aka soke zabukan su.

Yanzu hukumar zabe za ta bayyana ranakun da za ayi wannan zabe.

Saidai kuma tun a baya ma sanata Dino ya bayyana rashin amincewarsa da sakamakon zaben. Ya ce an yi magudi sannan an yi amfani da jami’an tsaro wajen muzguna wa masu zabe a wurare da yawa.

Share.

game da Author