A ranar Juma’a ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali matuka wajen inganta samar da kiwon lafiya ga yan Najeriya a kowani mataki.
Buhari ya bayyana haka ne da ya amsar rahotan kungiyar NIPSS a Abuja.
Idan ba a manta ba a watan Mayu ne Buhari ya umarci kungiyar NIPSS da ta yi bincike sannan ta tsaro hanyoyin da suka fi dacewa gwamnati ta bi domin samar da kiwon lafiya a kasar nan.
Buhari ya ce zai yi nazarin rahoton kungiyar kuma za a yi amfani da shawarwarin da ta bada sannan ya yaba da kokarin da kwamitin ta yi.
A karshe shugaban kungiyar Habu Galadima ya tabbatar wa shugaban kasa ingancin binciken da suka yi.
Galadima ya ce kungiyar ta gudanar da bincike domin gano matsalolin da fannin kiwon lafiyar kasar nan ke fama da su da hanyoyin da za abi don a gyara fannin sannan a samar wa mutane sauki wajen samun kiwin lafiya.
Sannan ta tattauna matsalolin da fannin kiwon lafiyar kasar nan da kwararun ma’aikata, masu ruwa da tsaki a fannin domin gano hanyoyin da suka fi dacewa wajen kawar da su.