Ina taya Dan-Uwana Mamman Daura murnar cika shekaru 80 – Shugaba Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murna ga Dan-Uwansa Baba Mamman Daura da ya cika shekaru 80 a duniya.

Buhari yayi addu’a da yi masa fatan Alkhairi a murnar bukin zagayowar ranar haihuwarsa.

Mamman Daura, wanda da’ ne a wajen shugaba Buhari ya cika shekaru 80 ranar 9 gawatan Nuwamba.

Mamman Daura, fitaccen dan Jarida ne wanda yayi aiki a jaridar New Nigeria a Kaduna har ya kai matsayin Manajin Darekta kafin ya bar aiki ya koma harkokin kan sa.

Ya kafa kamfanoni da dama da kuma hannu wajen kafa masaku a Kaduna.

Buhari ya jinjina wa Mamman Daura da kuma yi masa fatan Alkhairi.

Sunan Mamman Daura ya fito karara a labban ‘yan Najeriya ne tun bayan darewa kujerar shugabancin Najeriya da kawun sa ya yayi, wato Muhammadu Buhari.

Da dama cikin mutane harda uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari suna yi masa ganin sai yadda ya ke so Buhari yake yi.

A dan kwanakin baya an rika kai ruwa rana tsakanin mai dakin shugaba Buhari wato Aisha Buhari da iyalan Mamman Daura akan wani sashen damuna da suke zaune.

Aisha ta bukaci iyalan mamman Daura su kwashe kayansu su fice daga wannan sashe a Aso Rock domin danta ya shiga.

A wannan rana an kusa dambacewa a tsakanin su inda kowa ke kokarin nuna iko a wannan gida.

Ba shugaba Buhari ba kawai yan Najeriya da dama sun fito sun rika mika gaisuwar taya murnar cika shekaru 80 da Mamman Daura yayi.

Share.

game da Author