Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Ya ku ‘yan Najeriya, ya ku al’ummar Annabi Muhammad (SAW), kamar dai yadda kuka ji, kuma kuka sani, yau ranar alhamis, 21/11/2019, ranar murna ce da farin ciki a gare mu masoya Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, a duk inda suke a duniya. Yau wata kotu a Kano ta yanke hukunci na gaskiya, wanda da ma al’ummah suke jira, suke zato, suke tsammani, kuma suke sauraro. Ta rusa sarakuna guda hudu na bogi da Gwamnatin Jihar Kano ta kirkiro domin ta raba kan al’ummah, ta jefa gaba, hassada, da husuma tsakanin al’ummar Jihar. Wannan kotu mai albarka ta tabbatar wa da mutanen Jihar Kano, da ma duniya baki daya, cewa, lallai Sarki daya ne ake da shi a Jihar Kano, wato Mai Martaba, Magajin Dabo, Dan Lamido mai Allah, Malam Muhammadu Sanusi II. Ina rokon Allah ya ja zamanin Sarki, amin.
Lallai wannan hukunci ya kara tabbatar muna da cewa, har yanzu a kasar nan kotuna suna da tasiri, sannan kuma ya kara tabbatar muna da cewa, lallai akwai alkalai na Allah, Salihai, wadanda su kawai gaskiya ce a gaban su, ba abun duniya ba!
Muna rokon Allah, don tsarkin Sunayen sa, wannan alkali da ya yanke wannan hukunci na adalci, Allah ya kare shi, Allah ya daukaka shi, Allah ya taimake shi, Allah yasa ya gama da duniyar nan lafiya, amin.

Shi kuwa Mai Martaba Sarki, muna rokon Allah ya ci gaba da kare muna mutuncin sa da Martabar sa, shi da dukkanin sauran Sarakunan mu na Musulunci, amin. Dukkanin masu adawa da shi, saboda gaskiyar sa, da son ci gaban al’ummah, ina rokon Allah, idan masu shiryuwa ne, Allah ya shirye su, ya ganar da su gaskiya, su dawo kan hanya. Idan kuwa ba masu shiryuwa ba ne, ina rokon Allah yayi muna maganinsu, kamar yadda yake yin maganin duk wani azzalumi, amin.
Ya Allah muna gode maka, da wannan gagarumar nasara da ka ba mu.
Alhamdu lillahil-Lazi bi Ni’imatihi tatimmus-Salihaat.
Sannan don Allah, don Allah, don Allah, ina rokon dukkan wani masoyin Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, da yayi Sujudush-Shukri a duk inda yake, wato Sujadar godiya ga Allah da ya bamu wannan gagarumar nasara, ba don komai ba sai don nuna godiyar mu ga Allah Subhanahu wa Ta’ala.
Sannan masoyan Sarki wadanda ba Musulmi ba, wato Kiristoci, suna da damar yin godiyar su irin yadda addinin su ya koyar da su. Domin mun lura sosai cewa, Mai Martaba Sarki yana da masoya a ko’ina, saboda adalcin sa.
Sannan ina mai sanar da ‘yan uwa, cewa, zamu shiryar gagarumar walimah da addu’o’i da sauran su, domin kara godewa Allah Madaukaki akan wannan ni’imah da baiwa da yayi muna.
Zamu sanar da ku, rana, wuri da lokaci In Shaa Allahu idan mun gama tattaunawa.
Sannan daga karshe, muna sanar da manya, da ‘yan uwa, da shugabanni, da dukkanin matakan jami’an tsaro, kai da dukkanin wadanda abun ya shafa, cewa, mun samu cikakken labari na sirri da ke nuna cewa gwamnatin Jihar Kano da magoya bayan ta, da wasu bata-gari, suna nan suna shirye-shirye na harzukawa tare da zuga wasu mutane, don su fito, suyi zanga-zanga, su tayar da hankali, wai su nuna rashin amincewa da wannan hukunci da wannan kotu mai adalci da albarka ta yanke. Muna gani, kuma duk duniya ta shaida, cewa sanadiyyar hakan, har an samu wasu bata-gari a Karaye, sun fito, sun amsa wannan kira na marasa son zaman lafiya a Jihar Kano. Wanda wallahi, kowa yasan da cewa, wannan hukunci na kotu, da ya rushe wadancan masarautu na bogi da gwamnati ta kirkiro, shine ra’ayin kafatanin al’ummar Jihar Kano, da arewa, da ma ‘yan Najeriya baki daya, masu kaunar zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
Don haka, muna roko, duniya ta san da wannan, jami’an tsaro su san da wannan, sannan shugaba Muhammadu Buhari yasan da wannan. Wasu na nan suna kullen-kullen zuga magoya bayan su, don su rikita dan zaman lafiyar da ake da shi a Jihar Kano. Kuma da ikon Allah, Allah ba zai ba su nasara ba.
Ina rokon Allah, don tsarkin Sunayen sa, da ya tsare muna Jihar Kano, arewa, da ma Najeriya baki daya; ya bamu zaman lafiya mai dorewa, amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku,
Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa ta lamba kamar haka:08038289761.
Discussion about this post