HAWAINIYA: Yadda APC ta rikide ta koma PDP

0

Abubuwa hudu ne su ka sa jama’a dora wa jam’iyya PDP karan-tsana, a lokacin da ta ke kan ganiyar mulkin Najeriya. Na farko shi ne tabargaza da wawurar kudade da gwamnatin PDP ta rika yi, tun daga Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi.

Abu na biyu kuma shi ne kokarin da aka yi ta yi har karo uku a baya, domin tabbatar da Buhari ya zama shugaban kasa. Wannan ma ya taimaka wajen tsanar PDP. Saboda an rika ganin kawai idan Buhari ne ke mulki, to duk wata matsala, cikin kankanen lokaci zai iya kawar da ita. Kama daga wadanda ya gada zuwa wadanda za su iya bijirowa daga baya.

Na uku jama’a sun gaji da yadda a wancan lokacin ake harankazama wajen cin zabe a jihohi wajen zaben gwamna, sanata, tarayya har ma zuwa na shugaban kasa.

Inda darajar PDP ta kara yin kariyar da madora suka kasa dora ta, shi ne wajen sakacin da aka yi Boko Haram suka mamaye Arewa, kama daga birane, garuruwa, kauyuka, karkara da cikin dazuka, har da kan titi.

Buhari, wanda ya fara fafutikar neman zama shugaban kasa ya faro tare da wasu mutane masu rajin kishin kawo sauyi.

Sannu a hankali da rigingimu suka fara tirnike PDP, sai manyan ‘ya’yan ta suka rika canja sheka su na komawa ANPP, tun ma kafin ACN, CPC da APGA da ANPP su yi gambizar zama APC.

A na su bangaren, sanatoci da gwamnoni masu kammala wa’adin su duk sun taimaka wajen kara wa Barnon APC dawakai. Babu gwamnan da ke so bayan ya kammala wa’adin sa, kuma ya koma kofar gida ya na zaman-kashe-wando kan dakali. Don haka sai su da sanatoci suka rika yi wa duk wata jam’iyyar da Buhari ya ciki tururuwa.

Duk wanda sabon gwamna ya hana faffaka, sai ya fice daga PDP ya koma jam’iyyar da Buhari ya ke.

Kafin wani lokaci sai dandazon ‘yan PDP suka kewaye Buhari, suka zama bargon sa, rigar sa kuma alkyabbar sa.

Zugar da wasu gwamnonin PDP suka yi, suka koma APC, a karkashin jagorancin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da Bukola Saraki, ya kara wa tafiyar Buhari dandazon ‘yan PDP.

Za a iya cewa da karfin ‘yan PDP da kuma ACN ta bangaren su Bola Tinubu Buhari ya samu nasarar zaben 2015.

Ganin Buhari ya kama ragamar mulki, gaggan ‘yan PDP sun rasa uwa mahaifiya, sai suka rika komawa APC. Da tsohon mai laifi, da wanda EFCC ta baza karnukan ta don farautar neman sa, da mayun da sun ci dubu sai ceto, duk sai suka yi ta rankayawa APC.

Ta kai a yau a cikin gwamnonin APC, ‘yan asalin PDP sun fi yawa. Haka a cikin sanatoci da ministocin Buhari da mambobin majalisar tarayya duk gyauron PDP ne suka yi kaka-gida.

SALON MULKIN APC DA NA PDP

Duk da cewa an yi tsammamin ganin canji, da dama na ganin babu wani canji. Duk wani hobbasan da APC ke yi a yanzu, ita ma PDP ta taba yi.

Da yawa na ganin duk wata hauma-hauma musamman ta cin zabe da tsiya ko da tsinin tsiya, ita ma APC ta na yi, kamar yadda PDP ta rika yi.
Zaben gwamna a jihar Kano da na jihar Kogi da Bayelsa, sun kara zama ‘yar manuniya ga masu sukar Buhari.

Saukin da jama’a suka yi tunanin samu daga gwamnatin Buhari, sai wasu abubuwa suka bijiro musu a bazata. Yayin da aka yi fama da Boko Haram a lokacin Jonathan a Arewa, lokacin Buhari kuma masu garkuwa ne suka kassara Arewa, ciki kuwa har da jihar Buhari, wato Katsina, da yankin mahaifar sa, Daura.

Akasarin masu fada-a-ji a kewaye da Buhari, ‘yan PDP ne. Da yawan ministocin sa da sanatoci duk an zabe su ko an nada su a lokacin da su ke dauke da nauyin laifin zargin tabargazar da suka tafka a lokacin da su ke PDP.

A yau babu wani abu a cikin PDP, sai tuta mai launin lema mai kalolin ta fari da ja da kore. ‘Yan burbushin manyan da suka rage a ciki, akwai-ya-babu ne, wai hakorin zomo.

Duk wani jigo, gogarma, kasaitacce ko macijin-kaikayin cikin PDP, tuni ya rikide ya zama dan APC.

Share.

game da Author