Gwamnatin Najeriya ta biya kudi har dala milyan 200 ga kotunnIngila, a kokarin da Najeriya din ke yi na tsaida gurfanar da kasar daga tilasta ta biya kudin diyya na dala bilyan 9.2, wadanda kamfanin P&ID ke nema daga Najeriya.
Antoni Janar kuma Ministan Shari’ar Najeriya, Abubakar Malami ne ya shaida haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis.
Ya bayyana cewa biyan wadannan kudade da Najeriya ta yi, alama ce mai nuna cewa Najeriya ta dauko hanyar da kotu za ta jingine hukuncin da ta maka a kan ta cikin watannin baya.
Malami y ace Najeriya ce ta roki yin haka daga bangaren kotun, ita kuma kotu ta nemi Najeriya ta biya dala milyan 200 domin a dakatar da tilasta wa Najeriya biyan dala bilyan 9.2.
Sanarwar ta kara da cewa biyan kudaden a kotu, zai sa kotu ta fasa damka sammacen cire kudade daga asusu da kadarorin Najeriya da ke kasashen Amurka da Ingila.
Malami ya shi ma kamfanin P&ID ya amince da wannan yarjejeniya da aka kulla.
Sannan kuma sanarwar ta ce Malami ya ci gaba da bayyana cewa amincewa a biya kudin ya nuna cewa dama can kwangilar ta boge ce.
Sannan kuma wannan sanarwa ta kara nanata cewa Najeriya na ta matsa kaimin ganin an soke kwangilar ma gaba daya.
“Saboda a cikin makonnin da suka gabata, bincike ya ci gaba da nuna irin harkallar da aka kitsa a cikin rattaba yarjejeniyar aikin gas din wadda Najeriya ta kulla da kamfanin P&ID a shekarun baya, lokacin mulkin marigayi Umaru Yar’Adua.
Ya ce sakamakon abubuwan da aka fara bankadowa a yayin binciken da aka fara, a yanzu kuma Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin a yi bincike na kwakwaf, na game-gari domin bankado duk wani mai hannu a cikin wannan harkallar kwangila.