A dalilin haramta wa APC shiga zaben gwamna a jihar Bayelsa da Kotu ta yi, Hukumar Zabe ta Kasa ta bayyana cewa hakan ba zai hana ta gudanar da zabe a jihar ba kamar yadda ta shirya.
INEC ta ce za ta ci gaba da shirye-shiryenta cewa akwai sauran jam’iyyu sama da 40 da za a fafata da su. ” Saboda haka don an dakatar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC da ga takara ba zai hana sauran ‘yan takara fafatawa ba.” Kakakin Jam’iyyar APC na jihar Bayelsa Sarian Dangosu ta sanar da haka wa manema labarai a Yenagoa.
Idan ba a manta ba babbar Kotun Tarayya ta Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, ta haramta wa jam’iyyar APC shiga zaben gwamnan jihar wanda za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.
An sarkafa wa APC wannan haramcin shiga zabe ne kwana biyu kacal kafin shiga zabe.
Babbar Mai Shari’a Jane Inyang ce ta zartas da hukuncin a yau Alhamis, biyo bayan karar da daya dan takarar zaben fidda gwanin APC, Heineken Lokpobiri ya shigar, inda ya yi ikirarin an yi masa rashin adalci a zaben na fitar da gwani.
Tsohon Karamin Ministan Gona, Lokpobiri ya garzaya kotun ce ya nemi a tsige dan takarar da APC ta ce ta tsaida, David Lyon a maye gurbin da shi.
“Kotu ta yanke hukuncin cewa APC a jihar Bayelsa ba ta gudanar da zaben fidda gwamnin dan takarar gwamna a bisa ka’idar da doka ta rattaba ba. Don haka APC ba ta da dan takara a zaben na jibi Asabar.” Haka lauyan Lokpobiri Fitzgerald Olorogun, ya shaida wa manema labarai.
Sai dai kuma ya nuna damuwa sosai ganin an hana APC shiga zaben, ya na mai cewa ba haka su ka so ba.
Da aka tambayi lauyan abin da ya kamata ya yi, sai ya ce za su yi abin da ya dace, amma dai a halin da ake yanzu, APC ba ta da dan takarar gwamna a zaben gwamnan Bayelsa na jibi Asabar mai zuwa.
An dai zuba jami’an tsaro a kusa da kuma kewayen kotun. An rika binciken kowa har da ‘yan jarida kafin a bar su su wuce kotun.
Shi dai Lokpobiri, ya rika cewa ko ma yaya shari’a ta kaya, to a zabi APC, ko da kuwa ba shi aka ba takara ba.
Ya ce babu yadda za a yi ya fice daga APC ko da kuwa zabe bai yi kyau ba, domin ya ci arzikin jam’iyyar, ganin cewa har karamin ministan gona ya yi.
Abin dai ya zame wa APC bugu biyu kenan. Dama kuma ranar Talata da ta gabata, Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta tsige dan takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar APC a Bayelsa.
PDP ta kai karar sa cewa takardun da ya damka wa INEC dangane da bayanan sa da karatun sa sun ci karo da juna.
Ba wannan ne karo na farko da kotu ta hana jam’iyyar APC shiga zaben gwamna ba.
An haramta wa APC shiga zaben gwamnan jihar Rivers da na Zamfara a zaben 2019 da ya gabata. Wannan ya sa PDP ta lashe jihohin a bagas.
Discussion about this post