A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta shigar da kara ta na tuhumar shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa Amaju Pinnick da wasu shugabannin hukumar bisa zargin wawushe kudi har naira biliyan 4.
A lokacin da ake tuhumar Pinnick, an zarge shi da handame kudi har naira biliyan 4 wanda hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta baiwa Najeriya a dalilin halartar gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.
Saidai kuma tun a wancan lokaci da ake ta kai ruwa rana a tsakanin kwamitin da suka bankado wannan harkalla wanda gwamnati ta dora wa nauyin bincikar wannan harkalla da shugabannin NFF din.
A ranar Talata, Babar Kotu a Abuja ta yanke wannan hukunci inda maishari’a Ijeoma Ojukwu ta bayyana cewa a dalilin janye karar da gwamnati tayi sannan kuma bayan kotu ta gudanar da nata binciken ta gano cewa ita kanta karar bata da abin za a dogara da.
Kotu ta yi watsi kararrakin da suka kai 16 da aka shigar na tuhumar Pinnick da sauran shugabannin hukumar NFF din.
Discussion about this post