Jiya lahadi ne Gwamnatin Jihar Lagos ta karkame wuraren ibada har guda takwas da ke cikin Lagos, bayan an gargade su da karya dokar “cika kunnuwan jama’a da kara.”
Babbar Manajar Hukumar Tsaftace Muhalli ta Jihar Lagos, LASEPTA, wadda ita da kan ta ta jagodanci tawagar jami’an kulle gidajen ibadun, Dolapo Fasawe, ta ce an kulle wuraren ibadun domin ceto jama’a daga kamuwa da cututtukan da su ka ita dauka sakamakon al’amurran da ake gudanarwa a wuraren.
Babbar Manajar ta LASEPA, ta ce babu ja daba wajen garkame duk wani wurin ibadar da ya ki gudanar da lamurran sa kamar yadda doka ta shimfida, walau na Kiristoci ko na Musulmi, ko ma na wane addini.
Daga cikin wuraren ibadun da aka kulle, sun hada da: 68, Old Ota Road, Orile Agege; 4, Ademola Oshinowo Street, Off Love Street, Ketu; 1 Dele Amuda Street, Lekki.
Sauran wuraren ibadun da aka garkame, akwai mai lamba 17, Ajileye Street, Ilaje Bariga; 39, Kusenla Road, Elegushi da kuma Ajayi Bembe Street Abule Oja, Yaba.
Fasawe ta ci gaba da cewa tilas gidajjen ibadu da sauran jama’a su rika mutunta da al’adu da dabi’un sauran jama’a mabiya addinai daban-daban.
Ta kara da cewa abin da aka sani da gidajen ibada shi ne su nuna yin koyi da kyawawan dabi’u, kaunar juna, yarda da juna, ‘yan uwantaka da kuma kyakkyawar zamantakewa tsakanin makwauta.
Duk da haka ta nuna bacin rai ganin yadda wasu wuraren ibadu da suka hada coci-coci da kuma masallai ke haddasa rudani a cikin al’umma,
“Tunda mun sha yi musu gargaji, amma sun ki ji, daga yau duk wani coci ko masallacin da ya karya doka, zai yaba wa aya zaki.
“An sha rika cika wannan hukuma da kawo korafe-korafe da kukan yadda wasu wauraren ibada ke sakin layi daga tsarin da aka san addini ya gindaya sharuddan zamantakewa da juna a fadin jihar nan.
Ta ce duk da gargadin da aka sha yi wa wadannan wuraren ibada, duk bai shiga kunnen su ba.