Gwamnatin jihar Kano za ta ciyar da yaran makarantan firamare 6800

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar zata fara ciyar da yaran makarantar firamare 6800 dake karatu a makarantun jihar.

Gwamnati za ta ciyar da ‘yan aji 4 zuwa shida ne.

Ya fadi haka ne a taron kaddamar da shirin da aka yi a garin Jigirya ranar Litini.

A lokacin da aka fara ciyar da yara ‘yan makaranta, gwamnatin tarayya ta dauki nauyin yara ‘yan aji 4 zuwa 6 ne sai kuma yanzu da gwamnatin jihar Kano za ta dauki nauyin ci gaba da hakan wato na yara yan aji 4 zuwa 6.

Ganduje yace gwamnati ta yi haka ne domin karkato da hankalan iyaye da yara musamman ‘ya’ya mata wajen sanin mahimmancin samun ilimin Boko da na addini wanda hakan zai taimaka wajen hana talla da barace-barace a titunan jihar.

Ya kuma ce gwamnati ta kafa kwamitin da za ta rika sa ido wajen tafiyar da ilimi da ciyar da yara a jihar.

Ganduje ya yi kira ga attajirai da masu ruwa da tsaki da su hada hannu da gwamnati domin ganin wannan tsari ta zauna a jihar.

Bayan haka shugaban kwamitin sa ido na shirin ciyar da yaran Ya’u Yanshana ya ce gwamnati za ta ciyar da wadannan ‘yan makaranta abinci daga ranar Litini zuwa Alhamis sannan ranar Juma’a a bai wa daliban biskit da alawa.

Share.

game da Author