Gwamna Ortom ya yi wa bursunoni 500 afuwa

0

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya yi wa bursunoni sama da 500 afuwa a cikin shekaru hudu. Haka Kwamishinan Shari’a na jihar, Micheal Gusa ya tabbatar.

Gusa ya shaida wa manema labarai a jiya Talata a Makurdi babban birnin jihar cewa dukkan wadanda aka yi wa afuwar, ‘yan asalin jihar Benuwai ne.

Ya yi wannan jawabin ne jim kadan bayan kaddamar da Hukumar Bada Shawara kan Afuwa ta jihar.

“Daga cikin wadanda aka yi wa afuwa daga zaman kurkukun da su ke yi, har da wasu bursunoni 250 da aka tsare tare da ba su zabin biyan tara maimakon daurin da aka yi musu, amma suka kasa biya ballantana a sake su.

Sannan kuma akwai wasu da aka yi wa daurin rai-da-rai da kuma wadanda aka yanke wa hukuncin kisa.

“Su wadanda aka ci su tara suka kasa biyar, sai su ke zaman kurkuku, Ortom ya bayar da kudade, ya biya kudin tarar su, kuma an sallame su.

“Su kuma wadanda aka yanke wa daurin rai-da-rai an rage musu zuwa shekaru 10 wasu kuma shekaru 15.

Sai rukuni na uku su ne wadanda aka yanke wa hukuncin kisa. Su kuma an maida na su hukuncin zuwa daurin rai-da-rai.

Gaba daya dai a cewar sa mutane kamar 500 ne suka ci moriyar wannan afuwa.

Tun da farko, a lokacin da Ortom ke kaddamar da kwamitin, ya nuna damuwar sa matuka a kan yawan cinkoson daurarru a jidajen kurkuku na Makurdi.

Daga nan sai gwamnan ya ja kunnen matasa sun daina shiga harkokin aikata miyagun laifuka da nufin neman abinci.

Ya nuna musu cewa ita rayuwa ‘yar a hankali ce, kafin mutum ya kai ga matakin nasara, sai ya jajirce tukunna.

Daga nan ya shawarci kwamitin yi wa daurarru afuwa da su bincika su ci gaba da gano duk wadanda suka cancanci a yi musu afuwa, to zai yi musu, kamar yadda Sashe na 212 na Kundin Dokar Najeriya na 1999 ya tanadar.

Share.

game da Author