Karamin Ministan Harkokin Mai, Timipre Sylva, ya yi wa Gwamna Seriake Sylva godiya, amma a cikin shagube, kan yadda ya ce shi Sylva din ne ya haddasa yadda dan takatar gwamnan Bayelsa na APC, David Lyon, ya lashe zaben gwamnan jihar a cikin ruwan sanyi.
Sylva ya yi wa Dickson wannan godiya cikin shagube a lokacin da ya ke gabatar da zababben gwamnan na Bayelsa, Lyon ga Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Aso Villa, Abuja.
Ya ce rashin aiwatar da ayyukan raya jihar na a zo a gani da Dickson ya ki yi a jihar ne ya sa aka guji sake zaben PDP, aka zabi APC.
Zaben Kare-jini-biri-jini
An dai samu rahotannin tashe-tashen hankula daga ‘yan jaridu da kuma masu-zuba ido, da suka ce hakan ya lalata inganci da sahihancin zabukan na jihar Kogi da na Bayelsa.
Tuni dai fitattun Kungoyoyin Kare Dimokradiyya biyu, wato YIAGA da Situation Room, suka roki a gaggauta soke zabukan na jihohin biyu.
Sun ce an baddala sakamakon zabuka a cibiyoyin tattara sakamakon zabuka.
Ita ma Kungiyar CDD, ta ce ta tattara bayanan mutuwar mutane 10 da kuma wasu kusan 150 da aka ji wa raunuka a jihohin Bayelsa da Kogi.
Sai dai kuma Shugaban Kasa ya taya ‘yan takarar biyu da suka ci zabe murna, kuma ya jinjina wa jami’an tsaro dangane da aikin da suka yi a lokacin zabukan.
Ita ma APC ta ce sun samu gagarimar nasarar da jam’iyyar adawa da masu yada kalaman batunci har yanzu sun kasa dawowa daga hayyacin su, saboda mamakin yadda aka samu wannan gagarimar nasara.
Slyva ya ci gaba da yi wa Dickson shaguben cewa abin da ya yi kamar auren macen da ba ta kwarai ba ce, wadda dalilin ta zai hana ka sake samun iya auren matar kwarai.
“To Sylva bai rike auren da ya yi jihar Bayelsa da kyau ba, shi ya sa a wannan zaben al’ummar jihar suka yi watsi da shi, suka ki zaben sa.”
Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya roki duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben gwamnonin guda biyu ba, to ya garzaya kotu.
Discussion about this post