Mai Shari’a Uzor Anyanwu na Kotun Daukaka Kara, ya jaddada amincewa da hukuncin da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta yanke, inda ta bayyana cewa Sanata Abiodun Olujimi ta PDP ce ta lashe zaben Shiyyar Ekiti ta Kudu.
Bayan kammala zaben 23 Ga Fabrairu, sai INEC ta bayyana cewa Sanata na APC Adeyeye ne ya lashe zabe. Ita kuma Olujimi na PDP sai ta garzaya kotu ta nuna rashin amincewar ta. Lauyoyin ta suka fayace wa kotu cewa an tabka murda-murda a zaben.
Daga nan suka gabatar da kotu hakikanin adadin kuri’un da kowa ya samu, kuma suka nemi kotu ta soke zaben Adeyeyi, ta ba wanda suka shigar da kara a madadai ta,l wato Olujimi nasara.
A karar da ta shigar, Olujimi ta tabbatar wa kotu gamsassun hujjojin cewa ba a bi ka’idar da INEC ta gindaya wajen gudanar da zaben ba. An tabka harkalla da hauma-hauwa.
Daga nan sai ta roki kotu ta soke dukkan zabuka da aka gudanar a yankunan da aka tabbatar an tabka mata magudi.
Ta kuma zargi INEC da yi shakulatin bangaro wajen kin sa-ido sosai kan zaben. Kuma ta ce ejan-ejan na jam’iyyun siyasa ba su sa hannu a kan takardun zaben da aka yi amfani wajen kada kuri’a da sub a.
Guguwar tsigau ta tsige sanatoci da dama da mammbobin majalisar tarayya.
Yayin da a wasu shiyyoyi za a sake zabe, a wasu kuwa maye gurabun su aka rika yi da wadanda suka maka su kara a kotu.