Kungiyar Wadata Abinci ta Duniya, wato FAO, ta nuna matukar damuwa tare da shan alwashin hada kai da Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa, domin a dakile wasu kwayoyin cuta masu hana magunguna yin tasiri a jikin dabbobi.
Wakilin FAO a Najeriya, Sufyan Koroma ya bayyana haka tare da cewa wadannan kwayoyin cututtuka ba a dabbobi ne kadai suka zama makarai na maganin warkar da cututtuka ba. Ya ce har ma a cikin kayan gona.
Ya nuna damuwa matuka tare da nanata cewa irin yadda wadannan kwayoyin cuta ke hana magunguna shiga jikin dabbobi su kashe cuta, abin damuwa ne a a cikin kasashe, nahiyoyi da duniya baki daya.
“Wannan na ya sa shugabannin duniya suka yi kira ga Cibiyoyin da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya su tashi tsaye domin kawar da wannan damuwa a cikin duniya.
A cewar Koroma, akalla mutane 700,000 ke mutuwa a duk shekara a duniya, ta sanadiyyar wannan gagarimar matsala.
Ya kuma ce idan ba a tashi tsaye an kawar da ita ba, to fatara da yunwa ka iya kwantar da mutane milyan 24 nan da shekarar 2030.
Har ila yau, Koroma ya yi karin haske cewa ana amfani da tan 400 kacal a Afrika, a kowace shekara na magungunan kashe cututtukan dabbobi, amfanin gona da kamun kifi.
Amma ya ce ana nan ana kokarin a cewa a kowace shekara ana amfani da tan 105,000.