Hukumar EFCC ta karyata cewa ta janye zargin wawurar kudade da ta ke wa tsohuwar ministar harkokin man fetur, Diezani Alison-Madueke da sauran wadanda ake tuhumar su tare da ita.
Cikin 2018 ne EFCC ta maka Diezani da wani Dauda Lawal kotu. Lawal dai wani babban darakta ne a First Bank.
An zarge su da karkatar da dala bilyan 153 ana kusa da fara zaben 2015.
Baya ga wannan tuhuma da EFCC ta maka Diezani a kotu, har ila yau kuma ta na fuskantar wasu tuhume-tuhume na harkalla da wawurar makudan kudade.
Sannan kuma gwamnatin tarayya ta kwace wasu manyan kadarorin ta da suka kai adadin bilyoyin kudade.
Sai dai kuma har yanzu ba ta gurfana a gaban shari’a ba, ballantana ta kare kan ta, kasancewa tun bayan hawan gwamnatin Buhari, Diezani na Ingila, inda a can ma ta na fuskantar wani binciken karkatar da kudade ne.
Cikin wani yawabi da Kakakin Yada Labarai na EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, ya ce EFCC ta yanke shawarar raba caje-cajen da ta ke wa Diezani nec domin a kawo karshen jinkirin da ake samu wajen tafiyar da shari’ar.
“An kira karar wadanda ake tuhuma din har sau hudu. Amma daga ka ji an ce Lanre Adesanya ba shi da lafiya, ya na kwance hajaran-majaran, a asibitin Landan, sai a ce Nnamdi Okonkwo ya samu ciwon hawan jini, an kwantar da shi asibiti, sai kuma a ce wai Stanley Lawson ya gamu da hatsarin mota, ba ya iya zuwa kotu.
“A fili mu dai abin da muka fahimta kawai shi ne, duk wadannan uziri da suke bayarwa, wani shiri ne kawai don a kawo wa shari’a cikas.
“To domin kawo karshen wannan raini wayau ne sai EFCC ta yanke shawarar ta karkasa tuhumar ta su a kotu daban-daban” Cewar Uwujaren.
Discussion about this post