Hukumar EFCC ta gurfanar da wani dan damfara da ya yi amfani da sunan Shugaban EFCC Ibrahim Magu, ya yi kokarin damfarar daraktocin Hukumar NDDC.
Jami’an EFCC na shiyyar Fatakwal ne suka gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya ta Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Mutumin mai suna Robert Terfa Swem, an caje shi da laifin yin sojan-gona, ya nemi daraktocin Hukumar Raya Yankin Neja Delta, NDDC su ba shi makudan kudade, domin ya kai wa Magu, a fasa binciken su da ya ce musu EFCC za ta yi.
Mai Shari’a M.L Abubakar, ya tuhume shi da laifuka uku, kamar yadda mai gabatar da kara, Samuel Chime ya caje shi.
Mai sojan gonar dai ya shaida wa Daraktan NDDC, Anselm Agommouh cewa, Shugaban EFCC, Magu ne ya sa shi ya tattauna da su, domin a cire sunayen su daga wadanda EFCC za ta bincika dangane da tabargazar da ake bincike a Hukumar NDDC.
An zarge shi da yin sojan-gona, shirya 419 da kuma yin kazafin yi wa Magu karya, alhali Magu bai san wannan zance ba.
Mai gabatar da kara Samuel Chime ya roki alkali ya bada ranar da za a fara sauraren kara, amma a tsare dan damfarar a kurkuku.
Sai dai kuma lauyan sa mai suna Thaddacus Dzepe, ya nemi a ba shi beli, kuma mai gabatar da kara bai yi ja-in-ja ba.
Mai Shari’a ya bada belin sa a kan kudi naira milyan daya. Da kuma mutum daya da zai tsaya masa.
An dai damke shi ne a wani otal mai suna Juanita Hotel, a Fatakwal, lokacin da ya ke ganawa da daraktocin NDDC a madadin Ibrahim Magu da ya ce shi ya turo shi ya gana da su.
Discussion about this post