Jami’an Hukumar EFCC na Jihar Lagos sun damke Shugaban Gidan Kurkukun Kirikiri, kurkuku mafi girma a kasar nan.
An kama shugaban mai suna Emmanuel Oluwaniyi da wani babban likitan gidan kurukukun mai suna Hemeson Edwin, saboda samun su da aka yi da hannu wajen bada rahoton karya, wanda rahoton ne aka yi amfani da shi a matsayin hujjar da aka dauki rikakken dan damfara, Hope Aroke daga kurkuku, aka kai shi Asibitin Jami’an ’Yan Sanda, a matsayin majiyyaci.
Mutanen biyu da aka kama dai duk Mataimakan Kwanturolan Kurkuku ne, NSC da suka daure gindin rika fitar da Aroke kurkuku alhali ya na zaman daurin shekaru 24 a gidan Yari.
Cikin makon da ya wuce ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Hukumar EFCC ta bankado wani kasurgumin dan damfara, wanda ke tsare a kurkuku, amma daga can ya sake shirya yin wata damfara har ta dala milyan 1. Dala milyan daya dai kwatankwacin naira milyan 365 kenan.
Hope Olusegun Aroke ya shirya wannan sabuwar damfara ce daga kurkuku, inda ya ke zaman wa’adin daurin shekaru 24.
Ofishin EFCC na shiyyar Lagos, sun bayyana cewa sun bankado yadda aka yi wannan damfara ta cikin intanet, tare da amfani da wasu rikakkun ‘yan damfara da ke waje.
Sanarwar da EFCC ta fitar ta bayyana cewa akwai wadanda ake bincike dangane da zargin su da aikata laifukan damfara ta hanyar intanet, wadda aka fi sani da ‘cyber crime’.
“Bincike ya nuna ya shirya harkallar damfarar naira milyan 365 a lokacin da ya ke tsare a kurkuku, yana fuskantar daurin shekaru 24.”
Wadanda ya shirya harkallar tare da su, su ma an dade ana kokarin yadda za a kama su, tun kafin wannan damfara da suka shirya.
Daga kurkukun Kirikiri EFCC ta samu wannan labari, bayan da wani ya gulmata ma ta abin da ya faru.
Babban abin da ya fi daure wa jami’an EFCC kai shi ne yadda wannan kasurgumin dan damfara ya rika harkar damfarar sa daga cikin kurkuku.
Binciken farko da EFCC ta fara yi, ta gano Hope Aroke na amfani da internet da kuma wayar GSM a cikin kurkuku, abin da doka ta hana mai zaman kurkuku ya rika amfani da su.
A yau kuma EFCC ta Shiyyar Lagos, ta bayyana kama manyan jami’an gidan kurkukun su biyu, Olawaniyi da Edwin a jiya Litinin, 25 Ga Nuwamba.
Hukumar ta ce su biyun duk sun bada hadin kai wajen bai wa EFCC bayanai masu gamsarwa na rawar da kowanen su ya taka.
Tun a wancan makon dai PREMIUM TIMES HAUSA ta bayyana babban abin daure kai da al’ajabi kuma shi ne yadda Hope Aroke ya samu daurin gindin ’yan sanda, har ta kai ga an kwantar da shi Asibitin Musamman na Jami’an ’Yan Sanda da ke Falomo, Lagos.
Daga asibitin kuma saboda samun daurin gindin jami’an tsaro, sai Aroke ya rika fita ya na kama otal, inda matar sa da ’ya’yan sa kan je su gana da shi.
Har ma sai da ta kai ya rika zuwa ya na gudanar da wasu uziri da sha’anin gaban sa. Haka dai binciken da EFCC ta gudanar ya tabbatar.
A yanzu kuma EFCC na ci gaba da binciken ko su wa da su wa ne ke da hannu wajen rika daukar sa ana kwantar da shi asibitin jam’an ‘yan sanda, har ya na kama hotel, ya fice kuma ya shiga gari halartar wasu lamurran gaban sa.
Daurin Gindin Jami’an Tsaro
Saboda tsananin daurin gindi, bincike ya nuna Aroke ya na amfani da sunan gare, wai shi Akinwunmi Sorinmade, har ya bude asusun ajiya a First Bank da Guaranty Trust Bank.
Daga kurkuku kuma ya sayi gida a cikin rukunin gidaje na Fountain Spring Estate, Lekki, Lagos, a cikin 2918 a kan kudi naira milyan 22.
Sannan kuma ya sayi Lexus, motar alfarma samfurin RX 350 2018, wadda ya sai wa matar sa, Maria Jennifer Aroke.
Sannan kuma a cikin kurkukun ya na amfani da lambobin sirri na asusun cirar kudi na matar sa, wanda ya ke tura kudade kai-tsaye daga cikin kurkuku, ta hanyar amfani da wayar sa.
Ci gaba da binciken da ake yi kuma ya kara tabbatar da cewa a lokacin da ake cikin shari’a a 2015, Aroke ya sayi wani babban gida mai lamba ‘Plot 12, Deji Fadoju, Street, Rukunin Gidaje na Megamounds, a Lekki, Lagos, a kan kudi naira milyan 48.
Aroke dai daya ne daga wasu daliban Najeriya biyu mazauna kasar Malaysia da EFCC ta damke bisa laifukan damfara ta intanet a cikin 2012.
An kama su ne a wani gida mai lamba 1004, a Tsibirin Victoria Island, Legas.
Dan asalin garin Okene ne ta jihar Kogi, wanda ya tafi birnin Kuala Lumpur da karyar wai ya na karatun Kimiyyar Kwamfuta.
Sai dai kuma EFCC ta fallasa shi cewa babban gogarman wasu ’yan damfara ne ta intanet, wanda suka shahara da damfara a nahiyoyi biyu na duniyar nan.
Bayan an kama shi, an dade ana shari’a, daga nan dai Mai Shari’a Lateefa Okunno ta Babbar Kotun Jihar Lagos ta same shi da laifuka biyu, kuma nan take ta daure shi shekara 12 a kowane laifi daya.
Ya zama shekaru 24 kenan aka daure shi.
Discussion about this post