Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta shawarci Majalisar Dattawa da ta gudanar da zaman sauraren jin ra’ayin jama’a a kan kudirin kalaman kiyayya, kafin su yi gaggawar maida shi zama doka.
Kungiyar ta gwamnonin ta yi wannan kira ne cewa ya kamata majalisa ta karkata kan abin da ‘yan Najeriya ke so.
Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ne ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, bayan sun tashi daga taron da gwamnonin suka halarta, jiya da dare, a Abuja.
“Ni dai ko dau daya ban taba jin wani gwamna ko da guda daya ya fito ya ce ya na goyon kafa dokar hukuncin kisa a kan kalaman kiyayya ba.
Da aka tambayi Tambuwal ko me zai ce dangane da Dokar Karin Harajin VAT wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa, kuma ya nemi amincewar su, sai Tambuwal ya ce ya kamata ’yan Najeriya su rika fahimtar Buhari.
Ya ce gwamnoni na goyon bayan abin da zai kara samar da kudaden shiga ga gwamnatin tarayya, ta jihohi da kananan hukumomi.
“ Muna roko ga wadanda ba su fahimci wannan dokar karin kudin VAT daga kashi 5% zuwa kashi 7.5% ba, su sake bitar nazarin fahimtar abin sosai.
“ Wannan kasa da kuma jihohi mu na bukatar kudade sosai domin gudanar da ayyukan raya al’umma, bunkasa ilmi, inganta fannin kiwon lafiya da ma dukkan sauran fannonin rayuwa baki daya.
Dangane da wa’adin karshen watan Disamba da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta bayar cewa idan ba a fara amfani da sabon tsarin albashi ba, za ta tafi yajin aiki, Tambuwal ya ce kowace jiha na nan na ci gaba da tattaunawa da wakilan NLC na jihar domin a yi wa tufkar hanci.
“Na tabbatar cewa a na nan a na ta kokarin warwarewa. Nan da zuwa Disamba jihohi za su kammala shirya na su tsare-tsaren fara biyan sabon tsarin.