Dalilin tsadar shinkafar gida kudi daya da shinkafar waje – Masani

0

Wani masani da ke a Cibiyar Nazarin Shinkafa ta Afrika, mai suna Philip Idinoba, ya bayyana cewa dalilin da ke sa shinkafar da ake nomawa cikin Najeriya ta yi tsada daidai da wadda ake shigowa da ita daga kasar Thailand da sauran kasashe, shi ne saboda noman shinkafa da gyaran ta sun yi matukar tsada a Najeriya.

Da ya ke tattaunawa wa wakilin PREMIUM TIMES a Abuja, Idinoba ya ce hanya mai saukin karyewar farashin shinkafar cikin gida ita ce gwamnatin tarayya rika biyan manoman shinkafa tallafi, irin yadda ake biyan tallafin man fetur kawai.

Ya bayyana wa wakilin mu cewa, “noman shinkafa da aikin gyaran ta har zuwa daukar ta a kai ta kasuwa duk akwai matukar cin kudi a Najeriya.

“Kafin yanzu, gwamnati ta rika aiki a kan matakai uku: wato kara wa shinkafar da ake nomawa cikin gida inganci, kara yawan wadda ake nomawa da kuma inganta hanyoyin sarrafa ta.

“Misali, mai masana’antar rege shinkafa a Jihar Anambra, sai fa ya yi tafiyayya har jihar Neja, daga wannan kauye zuwa wancan, ya na sayen shinkafa samfarera da ba a gyara ba, sannan ya kai ta Jihar Ebonyi ko wata jiha makamancin haka.

“To tsadar kudin jigilar ta a mota ya yi yawa matuka. Sannan wadannan masu aikin rege shinkafar su tsaftace ta zuwa dura ta a buhunna, su na fama da rashin wutar lantarki da za su yi aiki da injinan su. Don haka tsadar aiki da janareton da suke yi na kara wa shinkafar tsada ita ma.

“Sannan kuma ba su da cikakkiyar kwarewar yadda ake aiki da wadannan injina. Da wata ‘yar matsala kadan ta faru, tilas sai sun nemo wani Ba’Indiye da ke aiki a Mikano wanda zai canja musu wasu bangarorin injin din su da ya lalace. Gaskiya su na fuskantar matsaloli masu girma da kuma yawan gaske.

Ya kara da bayanin cewa shi kan sa noman shinkafar akwai tsada kwarai. Sai ya buga misali da cewa kudin da manomi zai kashe wajen noma shinkafa hekta 1 tal sun yi yawa, idan aka kwatanta da shinkafar da zai samu a cikin noman hekta daya din.

Wannan kuwa a cewar sa, na faruwa ne saboda ba mu da hanyoyin noma na zamani da kuma kayan noma na zamani.

A cewar wannan masani, irin shinkafar da ake nomawa za a iya samun har tan 9 idan aka girbe ta. Sai dai kuma kamar yadda ya kara yin bayani, a nan kasar bai fi manomi ya samu tan 6 ba, saboda yanayin aikin shinkafar ban a zamani ba ne.

Daga nan sai ya ci gaba da bayyana hanyoyin ke sa ana samun asarar shinkafa a kadadar noman shinkafa mai yawa da kan lalace.

Ya kuma kwatanta bambanci yadda noman shinkafa ya ke tsakinin Arewa da Kudancin kasar nan. Sannan ya ce duk yadda shinkafar ka ta dauko yin kyau, to idan ba ka kula da ruwa, har ka bari ruwa ya rika shan kan ta, shikenan lalacewa za ta yi.

Ya yi kira ga gwamnati ta rage kudin takin zamani zuwa kashi 50 bisa 100 na farashin sa.

“Domin idan za ka sayi taki a kan naira 10,000, kuma za ka bukaci buhu shida, ka ga a taki kawai ka kashe naira dubu 60,000. To a dauka wajen noman ta ka kashe naira dubu 40,000. Tun a nan ka kashe naira dubu 100,000. Ba a ma zo batun girbi, cashewa da jigilar ta zuwa gida ko wurin gyarawa ba. Wadannan ma sai ka kashe makudan kudaden da da wahala ka samu wata ribar kirki, idan ma b aka fadi ba.”

Daga nan kuma ya yi kira da shigo da injinan gyaran shinkafa na zamani masu karanci kudi, a raba wa manoma. Hakan ma a cewar sa, zai kara ingancin shinkafar, tare kuma da saukake kudaden da ake kashewa wajen noman ta da aikin ta.

Yin haka a cewar wannan masani, zai sa farashin shinkafar gida ya karye, ta yi saukin farashi daidai aljihun talaka.

Share.

game da Author