DADIYATA: Rikakken mai adawa da Ganduje ya cika kwanaki 100 a hannun wadanda suka gudu da shi

0

A yanzu haka dai kusan zukatan iyalin Dadiyata sun fasa yin sanyi, ganin cewa matashin malamin jami’ar wanda ya yi suna wajen ragargazar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya shafe kwanaki 100 a hannun wadanda suka sungume shi a mota suka gudu da shi da karfin tsiya.

Dadiyata, wanda cikakken sunan sa Abubakar Idris, mai taratsi ne a soshiyal midiya, ya na bayyana ra’ayin sa wajen ragargazar Ganduje, an cukume shi aka jefa mota a cikin gidan sa aka arce, a cikin dare, ranar 2 Ga Agusta, a Kaduna.

Wasu sanye da hulunan da suka rufe fuskokin su ne suka kutsa cikin gidan sa a unguwar Barnawa, wajen karfe 1 na dare. Sun gudu da shi da motar sa, kirar BMW. Kuma har yau babu labarin sa ballantana labarin inda motar ta ke.

Dadiyata mai shekaru 34, malamin jami’a ne da ya yi suna wajen caccakar tafiyar tsare-tsaren mulkin Ganduje na Kano, amma kuma shi mazaunin Kaduna ne. Gwamnatin Kano dai ta nesanta kan ta daga sace Dadiyata da aka yi.

Duk da jami’an ‘yan sanda sun ce su na kokarin ganin sun gano shi kuma sun ceto shi a duk inda aka boye shi, yanzu dai ya cika kwanaki 100 cif da sacewa, kuma har yau babu shi babu labarin sa.

Kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam, ciki har da Amnesty International sun yi ta kiraye-kiraye da kakkausar murya ga gwamnati cewa ta tabbatar da ta ceto Dadiyata a duk inda ya ke.

Matar Dadiyata, Haneefa Idris ta bayyana wa PREMIUM TIMES ta waya cewa har yanzu ba su fidda ran za a ceto shi ba kuma zai kubuta. Kuma sun sha samun labari na ji-ta-ji-tar sa, amma da an bi labarin sai a ga ba sahihi ba ne.

Kakakin ‘yan sandan Kaduna Abubakar Sabo ya shaida wa PREMIUM TIMES a lokacin da aka gudu da shi cewa sace Dadiyata abu ne mai daure kai. Domin abin da suka sani, idan masu garkuwa ne, to bayan kwana daya ko biyu za su tuntubi iyalan wanda suka yi garkuwa da shi su nemi kudin fansa.

Amma batun Dadiyata har yau babu labari kuma wadanda suka gudu da shi ba su tuntubi kowa ba.

Sai dai kuma a yanzu da Dadiyata ya cika kwanaki 100 a hannun wadanda suka gudu da shi, PREMIUM TIMES ba ta samu jin ta bakin Kakakin ‘yan sandan na Kaduna ba.

Share.

game da Author