Kungiyar Rajin Kare Dimokradiyya ta CDD, ta bayyana cewa jami’an tsaro na da hannu dumu-dumu wajen barkewar rikici a wurare da dama a lokacin zaben jihar Kogi.
A ranar Litinin ne babban jami’in CDD, Jibrin Ibrahim ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai a Abuja.
Dama kuma PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda a gaban idon wakilan ta rikici ya rika barkewa da ke da alaka da sa hannun jami’an tsaro a barkewar rikicin.
Haka nan kuma jami’an tsaro sun rika yi wa jama’a barazana a ranar jefa kuri’a da kuma wurin jefa kuri’a.
Ibrahim ya nuna takaicin cewa jami’an tsaro da aka damka wa amanar kare rayuka da dukiyoyin jama’a, sun rika kai wa jama’a hari, har da shiga kakudubar satar akwatin zabe.
Sannan kuma ya nuna mamakin yadda aka ce an jibge jami’an tsaro masu yawan gaske a Kogi. Ya ce duk da wannan romon-kunne da aka yi wa jama’a, ba su ga wasu jami’ai na bincike a shingayen shiga da fita ba, sai dai dandazon ‘yan takife dauke da muggan makamai a kan titi, su ne ke aika-aikar su babu mai hana su.
Ya ce hakan ya nuna cewa gwamnatin jihar ta hada baki da jami’an tsaro aka yi dukkan ta’asar da aka aikata.
Ibrahim ya kara da cewa babu wani abu da INEC za ta iya yi, matsawar dai akwai matasa dauke da bindigogi samfurin AK47, ana barin su su na karakaina a rumfunan zabe.
Kungiyoyi da dama sun yi kira a soke zaben Jihar Kogi, wanda suka ce tashin hankali ne aka yi ba zabe ba.
Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Gwamna Yahaya Bello murna, kuma ya yaba da yadda jam’iyyar APC ta sake lashe zaben.