Wani likitan masu fama da ciwon siga mai suna Chima Adindu ya koka kan yadda yara kanana ke kamuwa da ciwon siga a kasar nan saboda sakaci na iyaye da sunan gata.
Adundu yace haka na da nasaba ne da rashin ciyar da yara abincin dake gina garkuwan jikinsu.
Ya ce rashin yin haka ne ke sa yara na yin kiba a jiki da kuma sa su kamu da ciwon siga.
“ A zamanin da idan kaji ance mutum ya kamu da ciwon siga amma yanzu yara kanana na kamuwa da cutar.
Adundu ya yi kira ga iyaye dasu mai da hankali ciyar da ‘ya’yan su abinci na gari wanda zai rika gina musu jiki.
Ciwon siga (diabetes) cuta ce dake kama mutum idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da muke ci a cikin mu wato Insulin.
Shi Insulin ya na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki.
Rashin aikin ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da ciwon siga.
Alamun wannan ciwo sun hada da yawan jin kishi, yunwa, yawan yin fitsari, kasala da dai sauran su.
Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar siga
1. Zuwa asibiti domin yin gwajin wannan cutar don sanin matsayin mutum.
2. A tabbata ana cin abincin dake taimakawa wajen inganta garkuwan jiki kamar su cin ganyayakin da ake ci da kayan lambu.
3. Mata za su iya shayar da ‘ya’yan su nono kamar na tsawon shekara biyu domin guje wa kamuwa da cutan.
4. A guji cin abincin dake sa kiba a jiki kamar su alawar cakulate,kayan zaki,giya,sigari,gishiri buredi da sauran su.
5. A riga motsa jiki da guje wa yawan saka kai cikin damuwa.