CAFKE JIGON APC: Magoya bayan jam’iyyar APC sun fito zanga-zanga a Gusau

0

A dalilin cafke tsohon mai ba gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari shawara kan muhimman ayyuka Ibrahim Danmaliki da gwamnatin jihar tayi ranar Litini, daruruwan magoya bayan jam’iyyar APC na jihar sun fito zanga-zanga a babban birnin jihar.

A ranar Litini ne jami’an tsaro suka waske da Danmaliki a bisa zargin tada zaune tsaye a jihar.

An zarge shi da ruruta wutar fitina a jihar bayan martani da ya maida wa gwamnatin jihar bisa zargin tsohon gwamnan jihar da tayi cewa yana mara wa mahara baya domin tarwatsa zaman lafiyar da aka samu a jihar.

Idan ba a manta ba Danmulki ya karyata bayanan gwamnan jihar Bello Matawalle na cewa da yayi wai tsohon gwamna AbdulAziz Yari yana yi wa harkar tsaro zagon kasa a jihar.

Ya kara da cewa tunda kotu ta ba PDP kujerar gwamnan jihar, ko babban birnin jihar bai taba zuwa ba iyakan shi Talatan Mafara, ma haifar sa.

” Ina so in tuna wa gwamna matawalle cewa ya tuna mutanen Zamfara ba su zabe shi fa. Kaf din su APC suka zaba saboda haka ya dai na ganin kamar cewa kamar shi wani abu ne.

” Yari mutum ne da ke da ilimin addini matuka sannan ya nada sanin yakamata. Babu yadda za ace wai yana shirya wa harkar tsaro jihar Zagon Kasa. Bayan ya sani zai gamu da Allah ranar gobe kiyama.

” Duk zaman lafiyar da Matawalle yake ta tallatawa wai an samu a jihar Zamfara, duk karerayi ne kawai. Har yanzu jiya-I-yau ne. Ana kashe mutanen jihar babu kakkautawa wanda mahara ke aikatawa amma yana fitowa ya rika shelar wai yayi kawo karshen matsalar.

Wannan martani da Danmulki yayi ya biyo bayan kalaman da gwamna Bello Matawalle ne yayi na zargi Yari da hannu wajen yi wa harkar tsaron jihar Zamfara zagon kasa.

Gwamnan ya yi wannan zargi ne ta hannun Kakakin Yada Labarai na gwamnan, Yusuf Idris.

Idris ya fitar da sanarwa, wadda ya sa wa hannu a madadin Matawalle cewa, Yari da magoya bayan sa na jinnhaushi da kishin irin zaman afiyar da aka samu a Jihar Zamfara, a karkashin Matawalle.

Ya ce an cimma yarjejeniyar samar da zaman lafiya tare da maharann da suka addabi jihar shekara da shekaru, a karkashin gwamnatocin da suka gabata.

“Tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari ba ya jin dadin zaman lafiyar da aka samu a jihar Zamfara, shi ya sa ya ke ingiza yaran sa su na yi wa tsaron jihar Zamfara barazana.”

Haka sanarwar ta bayyana a madadin Gwamna Matawalle.

Share.

game da Author