Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa sabuwar Dokar Tsarin Raba Ribar Danyen Man Fetur da ake hakowa a kasar nan hannu.
Wannan sabuwar doka dai tsohuwar doka ce tun ta 1999 aka yi ma ta kwaskwarima a yanzu, ta yadda kamar yadda Buhari din ya bayyana da kan sa, Najeriya za ta rika samun karin makudan kudade a bangaren hako man fetur.
Dokar ta ‘Production Sharing Contract’ (PSC) ta jibinci danyen mai da ake hakowa a cikin ruwa da kuma na kan tudu.
Idan aka fara amfani da dokar, kudaden shiga ta bangaren fetur zau karu sosai ga gwamnatin Najeriya.
Majalisar Dattawa ce ta mika wa Buhari kudirin dokar makonni biyu da suka gabata, shi kuma yau Litinin daga birnin Landan ya ma ta hannu.
A shafin Buhari na Twitter ya yi bayanin sa wa dokar hannu, cewa; “A wannan rana na sa hannun tabbatar da yi wa dokar Sabunta Raba Ribar Danyen Mai da ake hakowa a Nejeriya. Bari na yi amfani da wannan dama domin na gode wa Majalisar Dattawa saboda goyon baya da hadin kai da suka bayar wajen yi wa wannan doka kwaskwarima da kuma gabatar da kudirin na wannan doka.”
Haka Buhari ya bayyana, kamar yadda aka wallafa a shafin sa na Twitter, kuma Kakakin Yada Labaran sa, Garba Shehu ya kara yin bayani kamar haka din duk a yau Laraba.
Tsohuwar doka ce ta Jarjejeniyar Raba Ribar Mai Wanda ake Hakowa da aka kafa ta tun a ranar 23 Ga Maris, 1999, kuma tun a lokacin aka rattaba cewa za a fara aiki da ita tun daga can baya, wato a kan man da aka hako tun daga 1 Ga Janairu, 1999.
Doka ce da ta kunshi mu’amalar cinikakkyar raba riba tsakanin Najeriya da kamfanonin kasashen waje masu hako danyen mai a Najeriya.
Sai dai kuma an dade ana ja-in-ja, tankiya da tirka-tirka da kamfanonin hako man, su na nuna rashin amincewar su da kokarin da Najeriya ke yi na yi wa wannan doka kwaskwarima, tsawon shekaru masu yawa.
Gwamnatocin baya sun sha kokarin yi wa dokar kwaskwarima, amma wasu dalilai kan haifar da cikar tabbatar da kudirin har a amince da yi wa dokar kwaskwarima.
YADDA DOKA TA GINDAYA KA’IDOJIN YIN KWASKWARIMA
Sashe na 16 (1) na wannan doka ta ‘Deep Offshore and Inland Basin Production Sharing Contract’, wato Dokar Jarjejeniyar Raba Ribar Danyen Mai Da Ake Hakowa a Ruwa da Kan Tudu, PSC, ta tantance cewa:
Za a iya sake yi wa dokar kwaskwarima domin tabbatar da cewa an dan kara wa Gwamnatin Najeriya wani hasafi, a duk lokacin da farashin gangar danyen man fetur ya haura dala 20.
Manufar yin wannan kwaskwarima dai ita ce domin tabbatar da cewa an shata yarjejeniyar ta yadda Najeriya za ta rika amfana da kudaden ribar danyen mai da ake hakowa a kullum a cikin kasar nan. Sannan kuma ta yadda zai amfani tattalin arzikin kasar nan.
Buhari ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su ga canji sosai na karin samun kudaden shiga, ta yadda za a samu damar karin gina makarantu, asbitoci da sauran ayyukan inganta rayuwar al’umma.
Idan ba a manta ba, kwanan nan Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami ya dauko Dala ba gammo, inda ya nemi kamfanonin hako danyen mai a kasar nan su biya Gwamnatin Najeriya kudaden ariyar na ribar danyen mai da ake hakowa, har dala bilyan 62 da ba su biya ba tsawon shekara da shekaru, tun daga lokacin da farashin gangar danyen mai daya ta haura dala 20.
A yanzu dai farashin gangar danyen mai ya na lilo ne tsakanin dala milyan 50-60, kamar yadda Karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva ya bayyana kwanan baya.
Discussion about this post