Wani kaftin a sojin Najeriya ya gamu da ajalinsa bayan ya taka wayar wutan lantarki a jihar Yobe a wajen gumurzu da Boko Haram.
Wannan soja ya taka wannan wayan lantarki ne a daidai suna fafatawa da Boko Haram.
Mazunan garin Damaturu sun yi gudun ‘Takai-takai gobaran bera’yayin da Boko Haram suka far wa garin amma cikin lokaci kadan dakarun sojin Najeriya dake bataliya 233 tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan jihar Yobe suka fatattake su.
A ranar Juma’a da yamma wani kakakin rundunar sojin Najeriya ya tabbatar da mutuwar wannan soja.
Sai dai bai fadi sunnan wannan soja ba domin rundunar ba ta sanar da iyalan mamacin ba.
Harin da Boko Haram suka kai wa dakarun sojin a jihar Yobe ya auku ne bayan rundunar ta sanar cewa wasu tubabbun ‘yan Boko Haram guda 24 sun mika wuya.
Rundunar ta yarda da tuban ‘yan Boko Haram din ne bayan sun furta da bakinsu cewa sune ‘yan ta’addan da suka buwayi mutane tun a shekarar 2009.
A cikin adadin yawan wadannan mutane akwai mata guda Takwas.