BINCIKE: Kasashen duniya za su bukaci dala biliyan 264 don inganta rayuwar mata

0

Sakamakon binciken da majalisar dinkin duniya (UN) ta gudanar ya nuna cewa kasashen duniya za su bukaci akalla dala biliyan 264 don inganta rayuwar mata.

UN ta gabatar da wannan sakamako ne a taron inganta rayuwar mutane da samar da ci gaba na kasa da kasa da aka yi a kasar Kenya a wannan mako.

A lissafe dai kasashen duniya za su kashe wadannan kudade ne wajen inganta kiwon lafiyar mata musamman a wajen haihuwa hana yi wa ‘ya mace aure da wuri, hana cin zarafin mace da samar wa duk mata dabarun bada tazarar iyali.

Sannan za a yi amfani da wani kaso cikin wadannan kudade wajen daukan kwararrun ma’aikata a asibitoci, siyo magunguna da sauran kayan aikin da za a bukata domin inganta rayuwar mata da gudanar da bincike.

Shugaban UNFPA Natalia Kanem ta bayyana cewa kasashen duniya da dama sun gano cewa cin zarafin mata, yawan mace-macen mata da yara kanana da tsananin talauci ne matsalolin da suka addabi kasashe da dama a duniya musamman masu tasowa.

Ta ce wasu kasashen duniyan ma har sun tsara hanyoyin kawar da su amma karancin kudade ya hana hakan tabbatuwa

“Binciken UNFPA ya nuna cewa mata 800 ne suke mutuwa kulum a dalilin matsalolin da suka shafi daukan ciki da haihuwa, mata sama da miliyan 230 na fama da karancin dabarun bada tazaran iyali na zamani, kulum ana cin zarafin mace daya cikin mata uku sannan a kulum ana yi wa ‘yan mata 33,000 auren dole a duniya.

Shugaban kungiyar ‘Avenir Health’ John Stover ya ce saka yara a makarantan boko da koya musu sana’o’in hannu zai taimaka wajen kawar da duk wadannan matsaloli.

Babbar sakatariyar ma’aikatar aiyukkan kasashen waje na kasar Kenya Kamau Macharia ta ce amfani da wadannan kudade zai taimaka wajen rage yawan marayu da cutar da rayuwar mata a dalilin cin zarafinsu.

Share.

game da Author