BIDIYO: An yi wa wani da ake ‘zaton Buhari’ ne Kowa a Birnin Landan

0

Wasu gungun hasalallun matasa sun rika yi wa wani mota da a ke zaton shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne a ciki kowa a daidai zai fita da gidan Abuja dake Landan.

Babu wanda ya ga wanda ke cikin wannan mota sai dai tana dauke da lambar FGN 1 wato motar da ke daukar shugaban kasar Najeriya koma shugaban kasa ke amfani da ita idan yana Landan.

Matasan sun rika bin motar suna yi masa Kowa suna furta kalaman batanci sannan suna dukar motar da kwalayen da suke rike da su.

Wasu daga cikin kwalayen na dauke da rubutun ‘ A saki sowore dake tsare a hannun jami’an tsaron Najeriya” Wasu kuma suna dauke da kira da a saki shugaban kungiyar Shi’a na Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky.

Wadannan mutane dai dukkan su kotu ta yanke da a sake su bayan sun cika sharuddan belin da ta yanke musu saidai kuma gwamnati bata sake su ba haryanzu.

Matasan sun taru ne a gaban gidan Najeriya dake birnin Landan da ake kira gidan Abuja domin yin wannan zanga-zanga.

shidai wannan mota da ake zaton yana dauke da shugaba Buhari ya dan dakata domin masu zanga-zanga su bashi wuri bayan ya fito daga gidan kafin nan ya yi tafiyar sa.

Share.

game da Author