Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murnar sa ga sabon gwamnan jihar Bayelsa David Lyon bisa nasarar da yayi a zaben gwamna da aka yi a karshen makon da ya gabata.
Buhari ya kuma yaba wa ‘yan Najeriya kan yadda suka fito kwansu da kwarkwatar domin zabar gwaninsu a zabukan da aka yi.
A takardar da aka raba wa manema labarai wanda mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai Femi Adesina ya saka wa hannu Buhari yace ya yi kira da a rika kai zuciya nesa a lokuttan zabe a daina yawan tada husuma. Ya ce irin haka nuni ne cewa lallai akwai sauran gyara da za a yi nan gaba domin a rika samun zabe masu tsafta.
Sannan ya mika jajen sa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a lokacin zabe. Bayan nan ya yaba wa hukumar zabe bisa namijin kokari da tayi wajen gudanar da zaben.
Buhari ya yi kira ga zababben gwamnan jihar Lyon da ya rike jama’atai da kyawu sannan ya rungume kowa, ya kuma rangada wa jihar Bayelsa ayyuka na gari don ci gaban al’ummar jihar.
” Ba wai kawai an yi zabe an gama ba, duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba abinda ya fi dacewa shine ya garzaya kotu domin yin haka ne doka ta ce.”
Malamin zabe Faraday Orumwese ya bayyana sakamakon zaben ranar Litini inda ya ce Lyon ya doke abokin takarar sa da kuri’u sama da 100,000 . Lyon ya samu kuri’u 352,552, shi kuma Duoye Diri ya tashi da kuri’u 143, 172.