BAUCHI: Gobara ta yi wa ’yan jarida da dalibai ta’adi

0

Wata gobarar da ta tashi ranar Lahadi da rana, ta haifar wa dalibai da ‘yan jarida asara a Bauchi.

Gobarar ta tashi ne a gidan da suke zaune, a unguwar Gwalameji, gefen Bauchi.

Cikin wadanda suka yi asara, har da Abdul-Saheed Olaide, wanda shi ne wakilin Kamfanin Dillancin Labarai Najeriya, NAN.

Baya ga dalibai da ‘yan jarida, har ila yau gobarar ta ci kayan wasu da ke makwautaka da su.

Haka gobarar ta ci kayan David Adenuga, wakilin jaridar The Nation a Bauchi da kuma kayan wasu dalibai na Kwalejin Fasaha ta Gwamnatin Tarayya, da ke Bauchi.

Wadanda abin ya shafa sun bayyana cewa ba su san musabbabin tashin gobarar ba, wadda ta fara ci daga cikin dajin da ke bayan gidan su.

Sai dai kuma sun tabbatar da cewa wutar sai da ta lashe dakuna 9 kafin a kai ga kashe ta
Olaide ya ce gobarar ta lashe dukkan kayan aikin sa da sauran wasu kayan sa masu daraja.

Amma dai ya gode wa Allah tunda ya tsira da ran sa.

“Na gode wa Allah kasancewa wannan gobara ba cikin dare ta tashi ba. Kamar da wasa fa gobarar ta tashi. Mun yi asarar abubuwa da dama, wadanda ba ma zan iya bayyanawa ba a yanzu din nan.” Inji shi.

Shi ma Adenuga cewa ya yi dukkan satifiket din sa na makarantu da ayyukan da ya yi, duk sun kone kurmus.

“Ni a yanzu ma ban san daga ina zan fara ba. Ban san yadda zan yi ba. Ba ni da inda za ni. Ban da kayan da ke jiki na, ban tsira da komai ba.”

Wani mai suna Musa Sule da wutar ta tashi a kan idon sa, ya ce wajen karfe 1:30 na rana wutar ta tashi daga wani daki, a gidan kwanan na su mai suna Tinubu Lodge.

Ya ce Mi yiwuwa tukunyar gas ce musabbabin tashin wutar, domin akasarin dakunan duk akwai tukunyar gas a ciki. Kuma sun rika fashewa a lokacin da gidan ke cin wuta.

Daga karshe dai jami’an kashe gobara ne suka kai daukin kashe wutar.

Wata daliba mai suna Goodness Okpara, ta bayyana cewa ita ta na cikin coci gobarar ta tashi.

Share.

game da Author