Bashin naira tiriliyan 25.7 ake bin Najeriya -DMO

0

Ofishin Kula da Basussukan da ake bin Tarayya da Jihohi, ya tabbatar da cewa ana bin Najeriya bashin naira tiriliyan 25.7.

Babban Daraktar ofishin mai suna ‘Debt Management Office, Patience Oniha, ta bayyana haka a lokacin da ta ke jawabi a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya Mai Kula da Yadda Gwamnati Ke Kashe Kudade, wato, Public Account Committee, a Abuja.

“Ya zuwa watan Yuni, 2019 dai naira tiriliyan 25.7 ake bin Najeriya bashi, kudaden bashin sun hada da na tarayya da kuma na jihohi da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

“Mu na kiran wannan da sun a bashin bai-daya, kuma gwamnatin tarayya ce ta ciwo kashi 80 cikin 100 kudin.” Inji ta.

Oniha ta kara da cewa kashi 32 bisa 100 na wannann basuka duk a waje aka ciwo su, yayin da sauran kashi 68 kuma an ciwo su ne duk a cikin gida.

Ta ce Ofishin DMO ya fara aiki tun cikin 2000 bayan da gwamnatin lokacin ta yi kokarin da ya haifar da yafe wa Najeriya dimbin bashin da ake binta.

Ta kara da bayyana wa ‘yan kwamitin majalisar tarayya cewa Hukumar DMO ce ke da alhakin kuda da yadda ake karbowa da aikin da kudaden basuka. Sannan kuma ta na tsara karbo basuka a madadin Gwamnatin Tarayya.

“idan za ku iya lura, shekaru da dama kenan, kashi 85 na manyan ayyukan da ake aiwatarwa a cikin kasashen kudin kowace shekara, to ramto su Gwamnatin Tarayya keyi.

“Mu na karbo basuka daga bangarori daban-daban, da suka hada manyan kamfanonin kasashen waje, Babban Bankin Duniya, Islamic Development Bank, African Development, China Exim.

“A nan gida Najeriya kuma mu na cin basuka sosai. Kamfani zai yi aiki, amma sai a bas hi takardar yarjejeniyar za a biya shi rana kaza ga watan kasa.”

Daga karshe Oniha ta ce Hukumar ta ta DMO ba ta ajiye ko sisi daga aljihun ta a cikin kudin da gwamnatin tarayya ke ramtowa.

Ta ce ana ajiye su ne a Asusun Gwamnatin Tarayya a Babban Banki Najeriya, CBN, inda daga can ne za a rika biyan duk wasu ayyukan da ake aiwatarwa, wadanda aka ramto kudaden domin a yi su.

Shugaban Kwamitin, Hon. Wole Oke, ya ce daga yanzu Majalisa na bukatar kwafe-kwafen takardun bayanan basukan da ake karbowa.

Sannan kuma yace sun a bukatar kwafen bayanin kudaden basukan da gwamnatin tarayya ta ce za ta ciwo domin gudanar da ayyukan kasafin 2020.

Share.

game da Author