Ban taba tunanin juyin mulki zai yiwu a Najeriya ba – Yakubu Gowon

0

Shugaban mulkin soja na biyu a Najeriya, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya bayyana cewa bai taba tunanin cewa juyin mulki zai iya yiwuwa a Najeriya ba, kafin na ranar 15 Ga Janairu, 1966.

Bayan wannan kisa da aka yi wa shugabanni a ranar 15 Ga Janairu, 1966, Aguiyi Ironsi ya zama Shugaba na Sojoji, an sake yin juyin mulki biyar a kasar nan. Ciki kuma an dakile wasu ba daya ba.

Gowon ya zama shugaban kasa a ranar 29 Ga Yuli, 1966, bayan da kananan hafsoshin sojoji sun yi juyin mulki.

Hafsoshin sun ce sun yi juyin mulkin ne domin su yi ramuwar-gayyar kisan shugabanni da manyan sojojin Arewa.

Da ya ke tuna abin da ya faru a lokacin juyin mulkin, Gowon yace kafin sojoji su yi boren 15 Ga Janairu, 1966, bai taba tsamammanin juyin mulki zai faru ba a kasar nan.

Gowon ya yi wannan jawabi ne kwana daya bayan cikar ranar hairuwar sa shekaru 85 da haihuwa, a ranar 20 Ga Oktoba, wurin bikin nada shi da ba shi lambar girmamawa ta Shugaban Kungiyar ‘Civil Youth Society Group’.

“Ni kai nan a tsinci kai na inda ban yi tsammani ba. Da farko niyya ta na yi aikin soja har na kammala zamani na na yi ritaya. Amma wasu al’amurra suka wakana, wadanda ban taba tunanin za su iya faruwa ba” Inji shi.

Daga nan Gowon ya tuna labarin yadda aka rika tambayar sa batun juyin mulki a Najeriya, ya na cewa ba zai yiwu ba.

Hakan inji shi ya faru a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta dawowa Najeriya daga kwas na watanni shida da ya London. Ya ce sun dawo ne ta cikin jirgin ruwa tun daga London har Lagos.

Yakin Basasa

Gowon ne shugaban Najeriya a lokacin da yakin basasa ya barke, wanda ya haifar da kisan dubban jama’a da haifar da tarwatsa milyoyin al’umma. An shafe watanni 30 cur ana gwabza yaki tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan tawayen Biafra.

Da ya ke magana a kan wannan yakin, Gowon ya ce ko kungiyar Red Cross ta Duniya ta shaida cewa sojojin Najeriya ba su yi yaki da mugunta ko keta ba.

Sun yi yaki bisa yadda tsarin Yarjejeniyar ‘Geneva Convention’ ta gindaya.

“Dalili kenan sojojin Najeriya mu ka rika kare rayukan mata da kananan yara da ma duk wani da ya kasance dan Najeriya ne. Kuma dama hakan mu ke so a sake dunkulewa a zama daya.”

Ya kara nanata cewa ‘yan Najeriya da kuma gwamnatin sa ba ta da wata nifaka ko kiyayya ga kabilar Igbo.

“ Dalili kenan ma bayan yakin ya kare, ba mu yi murna ko bukukuwan yin nasara a kan mutanen da muka yi yakin da su ba.”

An dai kammala yakin cikin 1970, tare da bayyana cewa, “Babu wanda ya yi nasara, kuma ba a ci kowa da yaki ba.”

Gowon ya ce ya bayyana haka ne bayan kammala yakin domin dai a kara jaddada bukatar sake dinkewa da dunkulewa a matsayin kasa daya.

Share.

game da Author