Bamu da abinda za mu ce wa El-Rufai sai addu’o’i na Alkhairi – Sarkin Samarin Barnawa

0

Sanin kowa ne cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kan ziyarci garuruwan jihar da unguwannin Kaduna domin ganawa da jama’a da sanin matsalolin su kai tsaye tun bayan darewarsa kujerar gwamnatin Kaduna.

Hakan yasa a koda yaushe mutanen jihar ke yi masa fatan alkhairi da kuma addu’oin gamawa lafiya.

A ranar Juma’a 8 ga watan Nuwamba, gwamna El-Rufai ya garzaya unguwar Barnawa inda ya halarci sallan juma’a a fitaccen masallacin Juma’a dake Barnawa Low-Cost, Kaduna.

Gwamna El-Rufai tare da makarraban sa sun halarci sallan juma’a a wannan masallaci na Barnawa-Lowcost Kaduna.

Limamin masallacin, Malam Muhammad Imam Muhammad ne ya jagoranci gwamna da jama’ar tare da dimbin al’umman wannan unguwa a wajen Sallan Juma’a.

Bayan ya an idar da sallah, Imam Muhammad tare da na’ibin sa Imam Muhammed Bello Mai-Iyali, Malam Habib da sauran shugabannin wannan masallaci suka mika wa gwamna kyauta da kuma dan wasu koke-koken su da suke bukatan taimakon gwamnati a kai.

El-Rufai ya mika godiyarsa bisa karramawar da aka yi masa a wannan unguwa da masallaci.

Da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES Hausa, a garin Kaduna, Sarkin Samarin unguwar Barnawa da kewaye , AbdulAziz Mukhtar ya bayyana cewa wannan ziyara ya zo ne akan gaba.

” Babu abin da mutane Barnawa za su ce sai Allah ya saka wa gwamna da Alkhairi. Muna matukar godiya da wannan ziyara da ya kawo mana a wannan masallaci mai Albarka.

” Kaduna ta yi matukar dacewa da samun mutum mai hangen nesa irin gwamna El-Rufai. Duk abinda zai yi don jama’a ne sannan kuma talawa ne ke gabansa da kuma irin yadda ya cusa matasa a harkokin gwamnati. Muna godiya matuka.

” Yau idan ka duba, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Mohammed Abdullahi, matashi ne. Ba a taba yin haka ba. Muna yi masa godiya da kula da kuma ba matasa dama a gwamnatin sa da ya ke yi.

Share.

game da Author