Bakon Dauro: Za a yi wa yara allurar rigakafi a jihohi 19 na Arewacin Najeriya

0

Gwamnati za ta yi wa yara sama da miliyan 28 allurar rigakafi domin samar musu da kariya daga kamuwa da cututtukan bakon dauro da sankarau.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta sanar da haka ranar Lahadi a wata takarda da ta raba wa manema labarai a Abuja.

Za a yi wa yara allurar rigakafin ne a jihohin Bauchi, Benue, Borno, Kano, Katsina, Plateau, Taraba, Niger, Adamawa, Kaduna and Sokoto. Others are Gombe Jigawa, Kebbi, Nasarawa, Yobe, Zamfara, Kwara da babban birnin tarayya Abuja.

WHO, kamfanin hada magunguna ‘Gavi’, da Hukumar NPHCDA za su hada hannu da gwamnati domin ganin an yi wa yaran dake wadannan jihohi rigakafin.

Darektan hana yaduwar cututtuka da allurar rigakafi na NPHCDA Joseph Oter yace za a bi makarantu, tashoshi, kasuwanni, coci, masallatai da dai duk inda za a samu yara domin yi musu allurar rigakafin.

Manajan Darektan shirye-shirye na kamfanin ‘Gavi’ Thabani Maphosa ya bayyana cewa rashin yi wa yara allurar rigakafi na daga cikin matsalolin da suke fama da su.

Maphosa yace a Gavi a shirye take da ta tallafa wa gwamnati wajen ganin an yi wa duk yaran da ba ayi musu allurar rigakafi a kasar anan.

A watan Yulin da ya gabata, kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya yi kira ga kasashen duniya da su maida hankali wajen kiyaye yin allurar rigakafi a kasashen su.

Kungiyar ta yi wannan kira ne bayan binciken da ta yi tare da hadin guiwar asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) a 2018.

Sakamakon binciken ya nuna cewa har yanzu akwai akalla yara miliyan 20 da ko ba suyi alluran ba ko kuma ba su yi duka allurarn ba.

WHO ta ce cututtukan da ya kamata a fi maida hankali wajen yin allurar rigakafin su sun hada da bakon dauro, amai da gudawa da na dafin tsatsa ‘Tetanus’.

Share.

game da Author